Shugaban Hukumar PSC, Musiliu Smith Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Shugaban Hukumar PSC, Musiliu Smith Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

  • Tunda farko, ma'aikata a hukumar kula da ayyukan yan sanda, FSC, IGP Musiliu Smith (rtd) ya ajiye aikinsa saboda gazawa
  • Shugaban gamayyar kungiyoyi, bangaren PSC, Adoyi Adoyi, ya ce ma'aikatan da ke yajin aiki sun sha alwashin yin gaggarumin zanga-zanga idan Smith bai yi murabus ba kuma FG ta biya musu bukatunsu
  • A wani sabon cigaba a ranar Laraba, Smith, daga karshe ya saduda ya yi murabus daga mukaminsa, a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba

FCT Abuja - Shugaban hukumar kula da ayyukan yan sandan Najeriya, PSC, Musiliu Smith ya yi murabus daga aikinsa.

An tattaro cewa kwamitin hukumar ne ta bukaci Smith ya yi murabus kuma ya amince.

Sufeta Janar da Musiliu Smith
Shugaban Hukumar PSC, Musiliu Smith Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dubun Wani Kwararren Likita Dake Kashe Mutane Da Allura Saboda Manufa Ɗaya Ya Cika

Majiya ta yi ikirari

Wani kwakwarar majiya ya shaidawa Daily Trust cewa Smith, tsohon sufeta janar na yan sanda, zai mika mukamin ne ga tsohon alkali Clara Ogunbiyi da ke wakiltar bangaren shari'a a hukumar.

Kakakin Hukumar PSC Ya Tabbatar Da Murabus Din Musiliu

Ikechukwu Ani, mai magana da yawun hukumar, shima ya tabbatarwa wakillin majiyar Legit Hausa murabus din a wayar tarho.

Hukumar ta rika kai ruwa rana da ofishin sufeta janar na yan sanda kan wanene ke da hurumin daukan sabbin jami'an yan sanda.

Hukumar ta PSC ta tallata daukan sabbin jami'an yan sanda kuma ta bukaci masu sha'awan aikin su ziyarci shafinta na intanet su cike fom.

Amma, rundunar yan sandan ta bukaci al'ummar kasa su yi watsi da sanarwar, ta dage cewa rundunar ce ke da hurumin daukan sabbin jami'an yan sanda.

Hukumar PSC ta sanar da yajin aikin baba ta gani, ta bada dalili

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tukur Mamu Na Daukan Nauyin Yan Ta'adda, Inji Hukumar DSS

Hadakar kungiyoyin hukumar kula da ayyukan yan sanda, PSC, ta bada sanarwa fara yajin aikin sai baba ta gani ga mahukunta a hukumar kan rashin cika alkawari.

A cewar The Punch, kungiyar ta ce za ta fara yajin aikin daga ranar Litinin 29 ga watan 2022.

A cewar ciyaman din hadakar kungiyoyin, sashin PSC, Mr Adoyi Adoyi, ne ya sanar da hakan a hirar da aka yi da shi a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel