Kannywood: Wasu Shahararrun Jarumai Mata Da Aurensu Ya Mutu

Kannywood: Wasu Shahararrun Jarumai Mata Da Aurensu Ya Mutu

  • Ana yin aure ne don zama na har abada, sai dai akwai wasu matsalolin da idan suka kunno kai, rabuwar ce kadai ta ke zama maslaha
  • Ba a cikin jama’an gari kadai ake samun irin wadannan mace-macen auren ba, har a wurin fitattun jarumai na Najeriya ma ana samu
  • A wannan rahoton za mu kawo muku za mu bayyana fitattun jarumai wadanda aurensu ya mutu kuma suka ci gaba da harkokin rayuwarsu

Kowa yana yin aure ne don ya zauna har abada, amma bayan wani lokaci ana samu matsaloli iri-iri wadanda suke kawo cikas a auratayyar.

Ana samun mutuwar aure a wurin sanannun mutane na duniya, don haka ko a Najeriya ma ba a rasawa.

Labaran Kannywood: Wasu jarumai da aurensu ya mutu
Kannywood: Wasu jarumai mata da aurensu ya mutu. Hoto: Hausaloaded.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Akwai fitattun jarumai da suka yi aure kuma ya mutu wadanda suka ci gaba sana’o’i da sauran harkoki na rayuwarsu, ga wasu daga cikinsu kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

1. Asma’u Sani

Jarumar Kannywood din ta shiga masana’antar ne bayan aurenta na fari ya mutu. Ta samu daukaka mai yawa sakamakon yadda ta san aikinta a masana’antar.

Tana tsaka da samun daukaka ta yi aure na biyu, wanda sanadiyyar hakan yasa ta bar masana’antar to koma zaman aure.

An samu rahotanni akan yadda ta dawo masana’antar bayan auren ya mutu.

Ama’u Sani tana cikin jarumai matan da aka amsa hannu bibbiyu bayan aurensu ya mutu kuma aka ci gaba da sanya su a cikin shirye-shiryen fim.

2. Sadiya Gyale

Jarumar Kannywood, Sadiya Muhammad wacce aka fi sani da Sadiya Gyale ta bar masana’antar a shekarar 2015.

Sai dai aurenta ya mutu ne bayan cece-kuce ya yawaita akan abokatarta da wani jarumi na masana’antar, Baballe Hayatu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon buhunan abinci kamar yadda Buhari ya bada umarni

Sadiya Gyale tana cikin jerin jaruman Kannywood mafi kyau da aka taba yi a masana’antar.

Tsakanin 2011 zuwa 2015 ne aka nemi jarumar aka rasa a masana’antar, wanda daga bisani a shekarar 2015 ta fito fili ta gaya wa duniya cewa za ta auri masoyinta.

Sai dai auren bai wuce wata daya ba ya mutu. Tun bayan aukuwar lamarin, jarumar ta dauke kafarta daga masana’antar.

3. Fati Muhammed

Jaruma Fati Muhammed ta samu daukaka mai yawa a masana’antar Kannywood. Ta shiga masana’antar kusan shekaru 20 da suka gabata. Ta haihu sau daya.

Da farko ta fara auren Jarumi Sani Mai Iska ne, sai auren nasu bai yi tsawo ba. Ta dawo Najeriya bayan tarewar da suka yi da shi a Ingila wanda daga baya ta auri yayan Ali Jita.

Auren nasu da yayan Ali Jita bai yi tsayi ba, bayan shekaru kadan suka rabu.

A wata hira da aka yi da ita a Jaridar Blueprint, Fati Mohammed ta ce tayi nasara a rayuwa amma bata da sa'ar aure.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa

A wani rahoton, Musa Muhammad Abdullahi, da aka fi sani da Baba Musa, tsohon jarumi ne da ya fara fitowa a fina-finai tun kafin a kafa Kannywood kuma a yanzu yana cikin taurarin dirama mai dogon zango mai suna 'Kwana Casa'in.'

A hirar da Daily Trust ta yi da shi, ya yi magana kan batutuwa da dama da suka shafi karatunsa, aikinsa, masana'antar fim na Kano da Kaduna, sauye-sauye da aka samu da kallubalen da ake fuskantar ds.

Asali: Legit.ng

Online view pixel