Hajjin bana: Lokaci yana nema ya kure, har yanzu ba a dauki 50% na Maniyyatan Najeriya ba

Hajjin bana: Lokaci yana nema ya kure, har yanzu ba a dauki 50% na Maniyyatan Najeriya ba

  • Daga ranar Lahadi, babu wani jirgin da ya dauko Maniyyatan da za a bari ya sauka a Saudi Arabia
  • Har zuwa yanzu kusan 45% na wadanda suka biya kudin aikin hajjin shekarar nan ne aka dauka
  • Saudi ta ba Najeriya kujeru 43, 000 a shekarar bana, adadin wadanda suka iya tashi bai kai 20, 000 ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Kwanaki kadan suka rage a kammala jigilar maniyyatan wannan shekara zuwa kasa mai tsarki, amma har yanzu mutanen Najeriya su na gida.

Daily Trust ta ce daga cikin mutane 43, 000 da suka biya kudin aikin hajjin shekarar bana, wadanda aka dauka zuwa Saudi ba su kai rabi ba.

Har zuwa ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022, alkaluman hukumar kula da Alhazai ta NAHCON ta tabbatar da cewa maniyyata 19, 764 kurum suka isa Saudi.

Kara karanta wannan

Bata-gari: An kama 'yan mata 20 da samari 14 da ke rawar badala a jihar Gombe

Legit.ng Hausa ta fahimci 54% na wadanda suka yi niyyar sauke farali, su na gida. Ana tsoron wasu da-dama daga cikinsu ba za su samu zuwa a bana ba.

Kawo yanzu jiragen sama sun dauki maniyyata daga jihohi 23. Kano da Kaduna sun fi kowa yawan mahajjata a kasar, mafi yawansu su na nan a jibge.

Ranar Lahadi wa'adi zai cika

Umarnin da hukumomin kasar Saudi Arabia suka bada shi ne dole duk wani jirgin mahajjata ya isa kafin a fita daga ranar Lahadi 3 ga watan Yulin 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hajjin bara
Lokacin aikin Hajjin shekarar 2021
Asali: UGC

Da zarar wannan wa’adi ya cika, gwamnatin Saudi Arabia za ta rufe filin tashi da saukar jiragen sama ga wadanda za su zo da niyyar yin ibadar aikin hajji.

A yammacin Laraba aka bada sanarwar ganin jinjirin watan Zulhajji. A addinin musulunci, a cikin kwanakin wannan wata ne kawai ake yin aikin hajji.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Mutane 3000 za su rasa hajjin bana

Akwai mutane kusan 3000 da ba za su samu damar yin aikin hajji a wannan shekara ba saboda ba a iya kammala biya masu kudin daki a kasa mai tsarki ba.

Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa Saudi Arabia ba za ta karawa Najeriya yawan kujeru ba. Rahoton ya ce gwamnatin Saudi tayi watsi da bukatar NAHCON.

Kujeru 43, 008 aka ba Najeriya a wannan shekarara, daga ciki an ware 9, 032 domin masu kula da Alhazai. Ragowar kujerun ne za a bar wa sauran masu niyya.

Kudin Hajji ya karu

Tun a watannin baya ku ka ji labari hukumar National Hajj Commission of Nigeria ta yi hasashen akalla 50% zai karu a kan kujerar aikin hajjin da aka biya a baya.

Shugaban NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan ya nuna wadanda suka bada kudi za su ciko N1m. Dalili shi ne an samu canjin farashin Dala da karin harajin VAT.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel