Aikin Hajji zai tashi a shekarar bana, kudin sauke farali zai karu da fiye da 50% inji NAHCON

Aikin Hajji zai tashi a shekarar bana, kudin sauke farali zai karu da fiye da 50% inji NAHCON

  • National Hajj Commission of Nigeria ta yi hasashen akalla 50% zai karu a kan kujerar aikin hajji
  • Shugaban NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan ya nuna wadanda suka bada kudi za su ciko N1m
  • An samu canjin farashin Dala da karin harajin VAT daga lokacin da aka yi hajjin karshe zuwa yanzu

Abuja - Hukumar nan ta National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) mai kula da aikin Hajji a Najeriya ta ce kudin aikin wannan shekarar zai karu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan yana cewa hasashensu ya nuna kudin kujera zai karu da akalla 50%.

Abin da mahajatta suka biya a shekarar 2019 ya kai N1.5m. maganar da ake yi a bana, duk wadanda suka bada kudi tun 2020 sai sun cika akalla N1m.

Kara karanta wannan

Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Alhaji Zikrullah Hassan ya shaidawa shugabannin hukumar alhazai na reshen jihohi cewa matsalar tattalin arziki da wasu dalilai ne su ka jawo karin.

Hassan ya yi zama da jagororin da ke kula da aikin hajji a jihohi ne domin a fara shirin aikin bana.

Meya jawo farashi zai yi sama?

“Hasashenmu yana tashi sama saboda a shekarar 2019, a kan N306 aka canza Dala, amma yanzu Dala daya ta kai N410.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin Hajj
Musulmai na aikin Hajji a ka'aba Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images
“Mun kuma san cewa kashi 97% na hidimar aikin hajji, da kudin kasar waje ake amfani wajen abincin jirgi da sauransu.”
“Haka zalika kasar Saudi Arabia sun kara harajin VAT daga 5% zuwa 15%. Su na cewa sun kashe tulin kudi a Mina da Arafa.”

Tasirin COVID-19

Rahoton ya nuna cewa dole duk wani maniyyaci ya yi rigakafin cutar COVID-19 kafin ya sauke farali. NAHCON ta ce wannan zai jawo karin kashe kudi.

Kara karanta wannan

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

Hukumar za ta kawo tsarin da za a bi wajen yi wa masu shirin sauke farali alluran rigakafin cutar.

Kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana, tabarbarewar darajar Naira a kasuwa shi ne babban abin da zai yi sanadiyyar tashin kudin kujerar aikin hajji.

Za a ga sababbin tsare-tsare

Akwai bambance-bambance da za a gani a aikin hajjin shekarar nan. Sheikh Momoh Sulaiman ya bayyana wannan a wata hira da ya yi da Legit.ng Hausa.

Kwamishinan tsare-tsare, alkaluma, bincike da bayanai na hukumar aikin hajji ya ce wannan karo da na'urorin zamani za ayi amfani wajen aikin hajjin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel