Bata-gari: An kama 'yan mata 20 da samari 14 da ke rawar badala a jihar Gombe

Bata-gari: An kama 'yan mata 20 da samari 14 da ke rawar badala a jihar Gombe

  • Wata haramtacciyar rawar badala ta kai 'yan mata 20 da samari 14 ciki har da yara kanana hannun jami'an tsaron Najeriya
  • Kwamandan rundunar NSCDC a jihar Gombe ya ce ana amfani da sunan gidan rawar ne domin aikata karuwanci da neman ‘yan matan
  • Kwamandan ya bayyana damuwarsa da cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da yawaitar aikata laifuka a jihar da ma sauran su

GombeRundunar jami'an tsaron NSCDC reshen jihar Gombe a ranar Talata, 28 ga watan Yuni ta kama ‘yan mata akalla 20 da samari 14 da suka hada da yara kanana da ake zargi da aikata laifukan raye-rayen banza da aka fi sani rawar ‘Gidan lokachi’ ko kuma ‘Gidan gala.'

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

Da yake jawabi ga manema labarai a jihar, Kwamanda Waziri Goni, ya ce gidajen rawa na tasiri tabarbarewar tsaro, inda ya ce kawo yanzu rundunar ta rufe sama da 10 a fadin jihar, inji Punch.

Yadda aka kama masu rawar banjo a Gombe
Bata-gari: An kama wasu 'yan mata da samari da ke rawar badala a jihar Gombe | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, baya ga wannan rawar badala da aka ce ana yi ba bisa ka’ida ba, gidan nishadin ya kasance wata hanya ce ga ‘yan mata su koyi karuwanci, inda ya jaddada cewa da yawa daga cikinsu sun fito ne daga jihohi makwabta.

A wani bidiyo da muka samo daga Trust Tv, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Suna kiran wurin da Gidan Gala amma a gaskiya a daga kashe suna da samarinsu, za su tafi tare da su.
“Kashi 95 daga cikinsu matasa ne kusan shekaru 17, da kyar za ka samu ‘yan shekara 20 zuwa 22, kuma wurin ya dade. Ga masu su, sun yi rajistar wurin ne da sunan farfajiyar ciniki amma kuma yanzu suna aiki a matsayin otal da filin wasa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Kwamandan ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun yi aure ne kamar na mako guda, amma suke kashe auren ko su tsere su shigo jihar Gombe.

Ya kara da cewa:

“Sun fito daga jihohin Adamawa, Borno, Plateau, da Taraba. Yawancinsu ‘yan Arewa maso Gabas ne, daya ko biyu ne daga Kaduna da Jos, idan ba a magance wannan al’amari ba, zai yi zama mai hadari, ya kuma haifar da matsala ga daukacin al’umma.
“Wannan babbar barazana ce, wadannan abubuwa ne da ke haifar da satar mutane, fashi da makami. Wasu ana yaudararsu ana kashe su, wasu kuma suna fakewa da niyyar nishadi suna aikata laifi.”

Ba bakon abu bane samun masu kanan shekaru a gidajen gala

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya yi tattaki zuwa wani gidan wasannin nishadi da ke unguwar Bolari, Sabon Layi a jihar Gombe, sai dai bai samu damar ganin yadda ake rawa a gidan kasancewar da dare ake yi.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

Wani mai gadin gidan da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida masa cewa, akan samu masu kananan shekaru da ke fadawa irin wannan yanayi tabbas.

A cewarsa:

"Ana fara wa ne daga irin 8 zuwa 9 na dare haka, kuma har da maza masu shekaru da yawa na zuwa su ga yadda ake rawar sannan su watsa kudade.
"Da yawa 'yan mata ne kanana, kuma galibinsu ko dai gagararru daga gidajen iyayensu, ko kuma mata masu zaman kansu da ke da dakuna gidajen mata masu zaman kansu da ke kewayen unguwar.
"Kasan nan unguwa ce da ta yi kaurin suna, to ko 'yan sanda ma sukan karbi na goro ne kawai su tafiyarsu.
"Da daddare ka zo nan, nan ne za ka ga komai. Ni dai ka ga aiki na tsaron kofa."

Kalli cikakken bayaninsa:

Mata sana'a ta fi bani: Yadda mata ta gina gidaje da sana'ar toya 'Masa' a Gombe

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

A wani labarin, Misis Rebecca Dung, mai sayar da fitaccen kayan ciye-ciye a Arewacin Najeriya “masa” ta shawarci matasa da mata da su rika shiga kananan sana’o’i domin su iya rike kansu.

Dung, wacce ta ba da wannan shawarar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gombe, ta ce ta gina gidaje biyu daga kudaden da take tarawa a sana'ar sayar da kayan abinci a kusa da otal din Jiyamere da ke Gombe.

Matar mai ‘ya’ya uku ta bayyana cewa ta fara sana’ar masa ne shekaru 20 da suka gabata da mudun shinkafa daya bayan da ta koyi sana’ar a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel