Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zama don kallon jiragen kasa

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zama don kallon jiragen kasa

  • Wani matashi dan kasar Birtaniya, Francis Bourgeois, ya bayyana cewa ya yi murabus daga aikinsa domin ya zama cikakken mai kallon jiragen kasa
  • Matashin da ke da mabiya sama da 800,000 a Instagram a ko yaushe yakan tsaya kusa da layin dogo yana ihu da jin dadi yayin da jirgin kasa ya wuce
  • Jama’a da dama da suka mayar da martani kan lamarin nasa sun bayyana cewa ra’ayinsa mai kyau ne tunda yana sanya farin ciki a fuskokin mabiyansa

Burtaniya - Wani matashi mai suna Francis Bourgeois ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ya bayyana a shafukansa na sada zumunta cewa ya bar sana'arsa.

Matashin ya ce yanzu yana so ya yi amfani da cikakken lokacinsa ne kawai don ganin wucewar jiragen kasa. A halin yanzu babu wanda ya san ko zai sami wani aikin a gefe don biyan bukatunsa.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa
Matashi Francis Bourgeois | Hoto@francis_bourgeois43
Asali: Instagram

Ya shahara daga aikata wannan lamari

Da ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, matashin ya rubuta cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yau na bar aikina don yin aikin kallon jiragen kasa na cikakken lokaci na!"

A cikin gajeren bidiyon da ya fadi haka, matashin yana murmushi yayin da ya toshe kunnuwansa. Kafar Ladbible ta bayar da rahoton cewa, matashin ya shahara a kasar Birtaniya bayan da ya dauki sha'awar zama mai sana'ar kallon jirgin kasa.

Kalli bidiyon:

Mabiyan sa na kafar sada zumunta

Kullen Korona ne ta ba da gudummawa ga sha'awarsa na barin sana'a ya koma kallon jiragen kasa. Francis yana da mabiya miliyan 1.4 a TikTok da sama da 800,000 a Instagram.

Da yake magana da manema labarai kan sha'awarsa ga sana'ar kallon jirgi ya bayyana cewa:

"A makarantar sakandire, na dan danne sha'awata saboda ba abu ne sananne ba a duniya. Idan na shiga damuwa ko wani abu, lokacin da na ji sautin injuna suna kururuwa, ina jin dadi sosai."

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

Martanin jama'a

A kasa ga wasu daga cikin martanin jama'a a kafar Instagram:

stephen_brown_1983 ya ce:

"Ya sa ni murmushi sosai, farin ciki sosai. Kyakkyawan saurayi da wasa mai kyau fatan alheri a gare shi."

sampaulsenior5 ya ce:

"Shin ana biyan cikakken ma'aikacin kallon jirgin kasa?"

Pritchardswyd ya ce:

"Yana da kyau. Ina son ganin yadda yake jin dadi lokacin da jirgin ya yi ham. Ra'ayinsa abin ban sha'awa ne."

riskon1 ya ce:

"Madalla da ya sami farin cikinsa."

anoyantunginaka said:

"Ina fatan wani abu mai saukin da zai sa ni farin ciki, ya masa kyau!"

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

A wani labarin, wata motar kudi a Amurka ta haifar da wani babban al'amari yayin da daya daga cikin kofofinta ta bude kuma kudade daloli masu yawa suka watse a kasa.

Lamarin da ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, inda ya kawo tsaiko ga cunkoson jama’a a California, yayin da jama’a ke tururuwa domin kwasar rabonsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa

Da take nadar bidiyon lamarin, wata budurwa mai suna Demi Baby a shafin Instagram ta ce wannan shi ne mafi girman abin mamaki da ta taba gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel