Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi

  • Ciyaman din Kano Municipal, Fa'izu Alfindiki, ya jagoranci matasa sun tafi sun rusa wani wuri da Sha'aban Sharada ke aikin gini
  • Rahotanni sun bayyana cewa Sharada na son gina cibiyar koyar da sana'o'i ne a filin domin mutanen mazabarsa
  • Amma, Alfindiki ya bayyana cewa filin na gwamnatin jiha ne kuma Sha'aban bai nemi izini daga hukumomin da ya kamata ba, ya ce islamiyya gwamnati za ta gina

Kano - Rikicin siyasa da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano da Sha'aban Sharada, mai wakiltar Kano Munincipal a Majalisar Tarayya na kara kamari a yayin da Ciyaman din Kano Municipal ya yi jagoranci aka rusa filin da dan majalisar zai yi gini.

A watan Oktoba, an fara sa in sa tsakanin gwamnatin Kano da yan majalisar tarayya hudu a yayin da yan majalisar suka kai kara wurin uwar jam'iyya game da rikicin da ke faruwa a APC a Kano, rahoton Daily Trust.

Kano: Shugaban Karamar Hukuma Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi
Shugaban Karamar Hukuma a Kano Ya Jagoranci Matasa Sun Rusa Aikin Gini Da Dan Majalisa Ke Yi. Hoto: Fa'izu Alfindiki
Asali: Facebook

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen soshiyal midiya ya nuna yadda shugaban karamar hukumar Kano Municipal, Fa'izu Alfindiki ya jagoranci matasa sun rushe wurin da dan majalisar zai yi gini.

Bayan afkuwar lamarin, wasu mutane sun yi ta sukan lamarin da suka kira bita da kullin siyasa.

Wani shaida ya ce ciyaman din da wasu matasa ne suka tafi wurin suka rushe komai kamar yadda yya zo a ruwayar Daily Trust.

Ya ce:

"Sun isa wurin da ake aikin kuma ciyaman din ya fara karya allon sanarwar aikin kwangilar kafin sauran matasan suka taya shi rushe wurin.
"Sha'aban ya yi niyyar gina wurin koyar da sana'o'i ne domin mutanen mazabarsa."

Aikin ba gaskiya bane - Fa'izu Alfikdiki

Da ya ke martani, Fa'izu Alfinkdiki, ya ce Sharada bai samu izini daga kumar Kula da gine-gine da raya birane ta Kano, KNUPDA, ba kafin fara aikin.

Alfikdiki ya ce:

"Bai da izini daga wurin KNUPDA kuma bai tuntubi gwamnatin jiha ba.
"Akwai ka'idoji na amfani da filaye amma ba a bi su ba. Niyyarsa shine ya hada rikici tsakanin mutane da gwamnatin jihar.
"Filin na gwamnatin jihar Kano ne. Sai dai ya siya fili ya yi aikin ko kuma ya nemi izini daga karamar hukumar Kano Municipal ko Gwamnatin Jihar Kano."

Islamiyya gwamnati za ta gina a filin

Alfikdiki ya kara da cewa gwamnatin jihar ta tanada filin ne domin gina makarantar Islamiyya.

"Gwamnatin jihar za ta gina Islamiyya a filin. Kafin yanzu har zuwa yau, babu wanda ya tuntubi gwamnatin jiha ko karamar hukuma game da filin."

An yi kokarin ji ta bakin Sha'aban Sharada amma hakan bai yiwu ba.

2023: APC za ta tabbatar ta bawa Igbo takarar shugabancin kasa, Shugaban APC na Enugu

A wani labarin, Shugaban jam’iyyar APC, reshen jihar Enugu, Ugochukwu Agballah ya tabbatar wa da mutanen kudu maso gabashin Najeriya cewa jam’iyya mai mulki zata tsayar da dan yankin a matsayin dan takarar shugabancin kasa.

Agballah, ya yi wannan jawabin ne yayin tattaunawa da ‘yan jam’iyyar na mazabar Enugu ta gabas, inda ya ce APC ta yanke wannan shawarar ne cika wa ‘yan kabilar Ibo burin su na mulkar kasa, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel