Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

  • Wani faifan bidiyo da ke nuna mutane cikin annashuwa yayin da suke kwasar daloli da suka zubo daga wata babbar mota ya jawo cece-kuce
  • A cikin bidiyon, mutane sun bar motocinsu sun tsaya kwasar kudi a tsakiyar titi a California yayin da suka haifar da cunkoson ababen hawa
  • Masu amfani da shafin Instagram na Najeriya da suka mayar da martani kan faifan bidiyon sun yi mamakin dalilin da ya sa hakan bai faru ba a Najeriya ba

Wata motar kudi a Amurka ta haifar da wani babban al'amari yayin da daya daga cikin kofofinta ta bude kuma kudade daloli masu yawa suka watse a kasa.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, inda ya kawo tsaiko ga cunkoson jama’a a California, yayin da jama’a ke tururuwa domin kwasar rabonsu.

Kara karanta wannan

Bidiyon budurwar da ta kashe N657k don yin karin gashi mai jan kasa ya janyo cece-kuce

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka
Hotunan yadda ake kwasar kudi | Hoto: @demibaby
Asali: Instagram

Kowa ya sunkuya don kwasar na banza

Da take nadar bidiyon lamarin, wata budurwa mai suna Demi Baby a shafin Instagram ta ce wannan shi ne mafi girman abin mamaki da ta taba gani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bangare na faifan bidiyon ya nuna wani mutum da hannayensa biyu cike da daloli yayin da yake kururuwa cikin zumudi. Wani rahoto da Fox News ya fitar, ya ce an kama wasu daga cikin mutanen da suka kwashe kudin.

Kalli bidiyon:

Wasu sun mayar da kudin

A cewar wani rahoto da kafar yada labarai ta NBC ta fitar, hukumar ta FBI ta bayyana cewa, ko da yake wasu daga cikin mutanen da suka kwashe kudin sun mayarwa jami’an tsaro, an ga wasu suna tserewa da dalolin da ba nasu ba.

Lokacin da @instablog9ja ya sake yada bidiyon, a kasa mun tattaro wasu martani daga 'yan Najeriya:

Kara karanta wannan

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

tony.frank_ ya ce:

"Wannan irin abu na bukatar faruwa a 9ja bari na duba wani abu."

ice_rum_ yayi dariya:

"Dubi yadda duk suka yi kokari don taimakawa wajen kwashe kudin a kan hanya, irin wannan dan Adamtaka haka."

Milly_posh21 ya ce:

"Maimakon ki kwasa kin tsaya wani hira."

oluwatravis ya ce:

"Hmm kenan babu wanda yake da tsintsiya da Parker a mota?"

samspedy ya ce:

“Ya Ubangijin Najeriya, kar ka kaskantar damu."

vihkkies__couture ya ce:

"Ba sa kwasar abun nan yadda ya kamata."

Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayin da ya cika shekaru 64

A wani labarin, a ranar 20 ga watan Nuwamba ne tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 64, kuma abokai da masu fada aji sun hallara domin bikin tare da shi.

Domin murnar cikar dan siyasar shekaru 64, matarsa, Patience Jonathan, ita ma ta tabbatar da cewa ta nishadantar da shi da wata waka mai ban dariya.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

Yayin da ma'auratan ke cikin wani jirgin sama mai zaman kansa, Patience tare da wasu dangi sun rera wa Goodluck Jonathan wakar zagayowar ranar haihuwa. Duk da haka, muryar matar tsohon shugaban kasar ta fito fili fiye da na kowa yayin da take rera wakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel