Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

  • Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya ce bai san komai ba game da fastocin yakin neman zabensa na shugaban kasa da suka bayyana
  • Umahi ya ce watakila wadanda suka aikata hakan sun yi shi ne da zuciya daya
  • Sai dai ya ce ba zai taba tsayawa takarar shugaban kasa ba har sai Allah ya umarce shi da aikata hakan

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya nesanta kansa daga fastocin kamfen dake nuna cewa yana neman takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

An dai gano cewa fastocin gwamnan sun karade shafukan sada zumunta da wasu wurare a fadin kasar.

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana
Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana Hoto: Francis Nwaze
Asali: Facebook

Da yake martani kan lamarin a cikin wata sanarwa daga Francis Nwaze, mai bashi shawara kan harkokin labarai, Umahi ya bayyana cewa hakan na iya kasancewa manufa mai kyau.

Kara karanta wannan

Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista

Hakazalika, hadimin nasa ya ce gwamnan ya ce zai yi biyayya ga kiran da aka yi masa na tsayawa takarar shugaban kasa ne kawai idan har Allah ya nufe shi da yin haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwaze ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Gwamnan jihar Ebonyi ya kula da wasu fastocin yakin neman zabe a wayoyi dauke da suna da hotonsa da kuma rubutun “Injiniya David Nweze Umahi a matsayin shugaban kasa 2023” kuma sun yadu sosai a shafukan soshiyal midiya da Tashoshin Talabijin na yanar gizo, da kuma wurare masu mahimmanci a fadin kasar, don haka na zabi yin karin haske kamar haka:
"1. Cewa mai girma Gwamna bai ba da izinin yin wannan kamfen a madadin sa ba, sai dai kuma, Gwamnan ya fahimci cewa matakin na iya kasancewa da niya daya, hakan alamu ne na yarda da gogewa da basirar mai girma gwamna domin ya bayar da gudunmawa sosai a harkar. ci gaban kasarmu Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

"2. Cewa mai girma Gwamna, kasancewarsa mutum mai mutunta kundin tsari ba zai iya kaddamar da irin wannan gagarumin yakin neman zabe na ofishin shugaban kasa ba alhalin hukumar zabe bata riga ta bude kafar yin haka ba.
"3. Cewa Mai girma gwamna a matsayinsa na mai tsananin Imani da lokacin Allah zai jira Ubangiji ya bashi umurni sannan kuma sai dai idan Allah ya yi masa wahayi da ya tsaya takarar Shugabancin kasar, ba zai saurari kiran da aka yi masa ba.
"4. Cewa a halin yanzu Gwamnan ya shagaltu da samar da romon dimokuradiyya ga al’ummar jihar Ebonyi, gyara jihar bisa alkawuran da ya yi wa Allah guda biyar tare da gyara yankin Kudu maso Gabas da bayar da gudunmawarsa wajen gina kasa idan bukatar hakan ta taso."

A wani labari na daban, Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ya bukaci ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed da ya gaggauta yin murabus ko kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallame shi.

Kara karanta wannan

Yunwa: Satar tukunyar abinci a kan murhu ya zama ruwan dare a Enugu, Mutan jihar sun koka

Kiran da dan majalisar yayi martani ne ga sharhin da Mohammed yayi a baya kan kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020, kafin kwamitin binciken lamarin ya saki rahotonsa.

Rahoton kwamitin ya bayyana lamarin a matsayin kisan gilla sabanin matsayar Lai Mohammed na baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel