Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa

Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu yayin da bidiyon wani ango ya bayyana inda yake sharban kuka
  • An gano angon tare da mahaifiyarsa suna takara rawa a wajen liyafar bikinsa inda shi kuma ya dunga zubar da kwalla
  • Lamarin ya tsuma zukatan mutane da dama inda suke al’ajabin shakuwar da ke tsakaninsu

Tabas ranar aure na daya daga cikin ranaku mafi muhimmanci a rayuwar dan Adam, kuma kowani mutum yana da sigar da yake nuna yana cikin farin ciki.

Yayin da wasu kan nuna farin cikinsu ta hanyar dariya wasu kan fashe da kuka a duk lokacin da suka tsinci kansu cikin wata ni’ima.

Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa
Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa Hoto: sabiradio
Asali: Instagram

Hakan ne ya kasance da wani ango wanda ya fashe da kuka mai tsuma zuciya yayin da yake tare da mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

A cikin wani bidiyo da shafin instagram na sabiradio ya wallafa, an gano angon yana rawa tare da mahaifiyarsa inda ya dunga zubar da hawaye.

An kuma gano mahaifiyar tasa tana share masa hawayen da ke zuba daga idanunsa wadanda suka ki tsayawa. Ana haka kawai sai itama mahaifiyar tasa ta fara zubar hawaye.

Wannan lamari ya taba zukatan mutane da dama inda wasu ke jinjina irin shakuwar da ke tsakanin wannan ango da mahaifiyar tasa.

Har ila yau a cikin bidiyon, ana iya jiyo murnar jagoran taron yana shawartan angon da yayi ta maza amma kuma sai ya ci gaba da rera kukansa tunda suma maza suna da zuciya kamar kowa.

Bidiyon Ango Yana Sharɓar Kuka a Yayin Da Iyayensa Da Surukansa Suka Raka Shi Ɗakin Amarya

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Lamarin aure batu ne da ke tsakanin mata da miji amma wani ango ya kasa zuwa dakin amaryarsa har sai da iyayensa da surukansa suka yi masa rakiya har kan gado.

Kuma angon ya yi abubuwa masu ban dariya yayin da aka yi masa rakiyar lamarin dai kamar dirama.

A wani gajeren bidiyo da Wisdom Blog ya wallafa, angon tare da surukansa da 'yan uwansa sun shigo dakin amaryar da wayoyinsu domin daukan yadda haduwan farkon zai kasance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel