Sani Hamza
5178 articles published since 01 Nuw 2023
5178 articles published since 01 Nuw 2023
Kotun Majistare da ke Norman’s Land a Fagge, jihar Kano ta yankewa wasu 'yan TikTok 2, Ahmad da Maryam hukuncin daurin shekara 1 kan yada bidiyon batsa.
Majalisar Shira ta tsige shugaban karamar hukumar, Abdullahi Beli, da mataimakinsa bisa zarge-zargen rashawa. An nada Hon. Wali Adamu a matsayin mukaddashi.
'Yan siyasar Arewa sun bukaci Akpabio ya yi murabus daga shugaban majalisar dattawa bayan Sanata Natasha ta zarge shi da yunkurin yin lalata da ita.
Safiyanu Dalhatu ya kashe mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi. Yanzu dai 'yan sanda sun kama shi, sun kwace makamin, kuma ana shirin gurfanar da shi a kotu.
Mudashiru Obasa ya koma matsayin kakakin majalisar Legas bayan murabus din Mojisola Meranda, lamarin da ake ganin zai iya kawo karshen rikicin siyasa a majalisar.
Rt. Hon. Mojisola Meranda ta yi murabus daga mukaminta na kakakin majalisar jihar Legas, yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da addabar majalisar.
Charles Udeogaranya ya ce littafin Babangida ya share hanya ga samar da shugaban ƙasa daga kabilar Ibo a 2027. Ya nemi APC, PDP su tsayar da dan yankin a zaben.
Jami’an tsaro sun mamaye zauren majalisar jihar Legas a ranar Litinin, 3 ga watan Maris. Ana sa ran Meranda za ta yi murabus domin kawo karshen rikicin majalisar.
Mazauna Tarauni sun caccaki dan majalisa Muktar Yarima kan rabon dawa da gero a Ramadan, suna masu cewa ba doki ba ne da za su ci irin wannan tallafi.
Sani Hamza
Samu kari