Tirƙashi: Ƴan Sanda Sun Gano Ƙarin Bama Bamai 9 da ba Su Fashe ba a Kano

Tirƙashi: Ƴan Sanda Sun Gano Ƙarin Bama Bamai 9 da ba Su Fashe ba a Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta gano bama-bamai tara da ba su kai ga fashe wa ba a cikin kamfanin sarrafa karafa na Yongxing
  • Legit Hausa ta rahoto cewa an samu fashewar bam a kamfanin Yongxing a ranar Asabar bayan wani bam din UXO ya tashi
  • Bincike ya nuna cewa an shigo da bama-baman ne daga jihar Yobe a cikin kayan gwan-gwan, kuma fashewar ta yi ajalin mutum biyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa an gano bama-bamai tara (UXO) da ba su fashe ba a inda aka samu fashewar bam a ranar Asabar.

A ranar Asabar, Legit Hausa ta rahoto cewa an samu fashewar bam a kamfanin karafa na Yongxing da ke unguwar Mariri, kan hanyar Ring Road a Kano.

Rundunar 'yan sanda ta sake gano bama-bamai 9 da ba su fashe ba a wani kamfanin karafa a Kano
Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

An gano karin bama-bamai 9 a jihar Kano

Jaridar Punch ta ce fashewar da ta faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiya, kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata akalla goma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa wani bam ne da bai tashi ba a lokacin da aka so tayar da shi (UXO), shi ne yanzu ya haifar da fashewar.

Rundunar ta ce irin wannan bam din ne ya tashi a kamfanin ba wai wai bam din aka haɗa ba ne (IED), sabanin rahotannin da aka rika yadawa.

An gano irin wannan bam din na UXO guda tara a wurin; inda aka ga guda bakwai bayan fashewar, da kuma wasu biyu a yayin da aka tsananta bincike.

An gano daga inda bama-baman suka fito

A cewar wata sanarwa da DSP Hussaini Abdullahi ya fitar, binciken da sashen kula da bama-bamai (EOD-CBRN) na rundunar, ya nuna cewa shigo da bama-baman aka yi.

DSP Hussaini ya ce sashen EOD-CBRN ya gano cewa an taho da bama-baman UXOs ɗin ne daga jihar Yobe a cikin kayan gwan-gwan, ba tare da masu kayan sun san da su ba.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa babu wata barazanar tsaro a Kano
Kwamishinan rundunar 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori tare da wasu jami'an tsaro. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Binciken 'yan sandan ya kuma nuna cewa dayan daga cikin bama-baman ya fashe ne a lokacin da ake sauke waɗannan kayayyakin a kamfanin ƙarfen.

Kwamishinan 'yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori ya jagoranci tawaga wajen da abin ya faru, inda suka tabbatar da tsaron wurin da kuma kwashe sauran UXO da ba su tashi ba.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano don samun magani, inji rahoton jaridar Leadership.

Rundunar 'yan sanda ta kore batun kai hari

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun karyata cewa bam ne aka dasa da gangan a Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyar.

Rundunar ta tabbatar da cewa bama baman UXO ne aka shigo da su jihar a motar 'yan gwan-gwan, kuma makamai ne na soja waɗanda ba su tashi ba.

Kwamishinan ya miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa kuma ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankulansu, yana mai tabbatar musu cewa babu wata barazanar tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.