‘Fetur Zai Ƙara Tsada': IPMAN Ta Faɗawa Ƴan Najeriya Illar Yaƙin Iran da Isra'ila
- Litar fetur a gidajen mai a Najeriya ta kusa kai N1,000, sakamakon rikicin Iran da Isra'ila da ya haifar da tsadar farashin ɗanyen mai
- Farashin man Brent da WTI sun ƙaru tun bayan fara rikicin, inda suka kai kololuwar tsada sakamakon tashin hankula a Gabas ta Tsakiya
- IPMAN ta shawarci 'yan Najeriya da su shirya wa ƙarin farashin, yayin da KB Mai Aski ya bayyanawa Legit Hausa damuwarsa kan farashin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gidajen man fetur a fadin Najeriya sun fara sauya farashin litar man fetur, inda yanzu ke sayar da litar kusan N1,000.
Wannan karin farashin ya biyo bayan hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, sakamakon rikicin da ke kara tsananta tsakanin Isra’ila da Iran.

Asali: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, dillalan mai sun shawarci ‘yan Najeriya da su shirya wa karin hauhawar farashin muddin ba a samu saukin rikicin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa tun bayan barkewar rikicin, an lalata muhimman kayayyakin mai, lamarin da ya haddasa tashin gwauron zabo na farashin danyen mai a duniya.
Tashin farashin danyen mai a duniya
Daga lokacin da rikicin ya fara, farashin ɗanyen man Brent ya tashi da 11.71% daga $66.45 zuwa $74.23, inda ya kai har $78.50 – mafi ƙololuwa tun 27 ga Janairu.
Haka zalika, a karshen makon da ya gabata, farashin danyen mai na U.S. West Texas Intermediate (WTI) ya kai $72.98 kan kowace ganga, karin $4.94 ko 7.62%.
WTI ya tashi da fiye da 14% zuwa mafi ƙololuwar farashi tun 21 ga Janairu da aka sayar da shi a kan $77.62, bayan karin 13% daga makon da ya gabata, inji rahoton Mayala Business Insight.
Rikicin Isra’ila da Iran ya kara dagula harkokin kasuwar man fetur, inda masu zuba jari ke cikin fargaba sakamakon rashin tabbas da rikicin Gabas ta Tsakiya ke haddasawa.
A ranar Lahadi, farashin danyen mai ya tsaya a sama da $77 kan kowace ganga, duk da ya sauko daga $79 da ya kai a karshen mako.
Fargabar farashin mai bayan harin Amurka
Akwai fargabar karin farashin man bayan Amurka ta kai farmaki kan wasu cibiyoyin makamashin nukiliya uku na Iran, yayin da Iran ta sha alwashin daukar fansa.
Masana sun ce daukar fansa daga Iran na iya haddasa karin hauhawar farashin danyen mai, kamar yadda rahoton Bloomberg ya nuna.
A matsayinta na kasa ta uku mafi samar da danyen mai a duniya, Iran na da fiye da kashi 24% na man fetur a Gabas ta Tsakiya, da fiye da 10% a duniya baki daya.
Duk da cewa karin farashin danyen mai na nufin samun karin kudaden musayar waje ga Najeriya, hakan na nufin karin farashin man fetur a cikin gida, kuma masana da dillalan mai sun ja kunnen ‘yan Najeriya da su shirya wa karin.

Asali: Getty Images
‘Yan Najeriya su shirya' – IPMAN
Da yake zantawa da manema labarai, Jami’in hulda da jama’a na ƙasa na kungiyar dillalan man fetur (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya bukaci ‘yan Najeriya da su shirya wa karin farashi.
Ya dora alhakin karin farashin a kan “tsananin hauhawar” farashin danyen mai sakamakon rikicin Isra’ila da Iran da ke gudana.
Ya ce hatta ita ma matatar Dangote ba za ta iya sayar da mai kasa da farashin kasuwa ba, duk da yarjejeniyar cinikayyar danyen mai a Naira.
“Dangote zai bi ƙa’idojin OPEC ne. Ba wai ana ba shi danyen mai kyauta ba ne,” inji Chinedu Ukadike.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta rage farashin fetur a nan cikin gida domin rage radadin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon karin farashin man a duniya.
"Galan ya kai N4,800" - KB Mai Aski
Legit Hausa ta tattauna da Alhaji KB Mai Aski, wanda ya nuna korafinsa kan yadda tun yanzu farashin man ya fara karuwa a Kaduna.
A cewar KB Mai Aski:
"Dazu na fita na sayo fetur wajen masu bunburutu, ka san muna da nisa da gidan mai, idan ina a gaggauce, wajen 'yan bunburutu kawai nake saya, to da na je, kwata N1,200 suke sayar da ita.
"Ka ga galan zai tashi N4,800 kenan. Wannan ba karamin tsada ya yi ba. Na ji an ce a gidajen man ma farashin lita ya haura N950. Kawai sai dai mu roki Allah ya ba mu halin siye."
NNPCL ya kara farashin fetur a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin NNPCL ya kara farashin kowace litar man fetur a gidajen mai da ke ƙarƙashinsa a faɗin ƙasar.
An lura da wannan ƙarin a gidajen mai mallakin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da ke manyan biranen Abuja da Legas.
A babban birnin tarayya, wato Abuja, an ruwaito cewa farashin kowace litar man fetur ya koma N945, saɓanin N910 da ake sayarwa a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng