Netanyahu Ya Bijirewa Umarnin Trump, Ya ba Sojoji Umarnin Kai wa Iran Hare Hare
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna bacin ransa ga Benjamin Netanyahu bayan da Isra'ila ta kai sababin hare-hare hari kan Iran
- Tun da fari, sai da Trump ya gargadi Isra'ila da kada ta ƙara kai hari Iran, amma ta ki ji, lamarin da ya rusa yarjejeniyar tsagaita wuta
- Rahotanni sun nuna Trump na jin cewa kamar Netanyahu ya yaudare shi, bayan ƙoƙarin da ya yi na sulhunta tsakanin ƙasashen biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nuna matuƙar bacin ransa ga Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran.
Wannan lamarin ya jefa shakku kan ƙoƙarin da Trump ya yi na samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar yarjejeniyar tsagaita wuta.

Asali: UGC
Kiran wayar Trump da martanin Netanyahu
Kafin sanar da yarjejeniyar tsagaita wutar, Trump ya bayyana cewa ya kira Netanyahu kai tsaye domin roƙonsa da kada ya ci gaba da kai hari kan Iran, inji rahoton Sky News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, a cewar Netanyahu, Iran ta riga ta karya yarjejeniyar, don haka dole ne su mayar da martani, koda kuwa da hari guda ɗaya ne kawai.
Trump ya nuna fushinsa sosai kan harin Isra'ila, domin sai da ya gargadi Netanyahu a shafinsa na Truth Social, inda ya ce:
"Isra'ila, ka da ku saki wadannan bama baman. Idan kuka yi haka, to kun karya yarjejeniyar da aka yi. Ku gaggauta dawo da jiragenku gida."
Ya ƙara da cewa bai ji dadin yadda Isra’ila ta saki bama-bamai a Iran ba a kasa da sa’a guda bayan amincewa da tsagaita wutar.
"Lokacin da na ce kuna da sa’o'i 12 na shigar yarjejeniyar, ban fadi haka don ku fara sakar masu dukkanin bama baman ku a kan su awa ɗaya ba," in ji Trump cikin ɓacin rai.
Trump ya yi zagi a kan rikicin Iran da Isra'ila
A cewar Trump, Iran da Isra’ila sun shafe shekaru suna yaƙi har sun daina gane yadda za su dakatar da rikicin.
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya fusata sosai har ya yi zagi yayin da yake bayyana fushinsa kan keta yarjejeniyar.

Asali: Getty Images
Mun ruwait cewa Trump ya bayyana cewa duka ƙasashen biyu sun karya yarjejeniyar tsagaita wutar, amma ya jaddada cewa fushinsa ya fi yawa a kan Isra’ila.
Wani rahoton Al Jazeera ya nuna cewa Trump na jin cewa Netanyahu ya yaudare shi, kuma yana jin takaici da bacin rai a kansa.
Kafin haka, Trump ya ce ya nemi taimakon Qatar domin samun amincewar Iran bayan da ya riga ya samu goyon bayan Netanyahu kan shirin tsagaita wutar.
Wannan rikicin da ya sake ɓarkewa ya mayar da yunkurin sulhu baya, duk da ƙoƙarin Trump na hana ci gaba da rikicin.
Iran ta kai hari Isra'ila bayan tsagaita wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ta samu matsala, bayan Isra’ila ta zargi Iran da harba mata makamai.
Ministan tsaron Isra’ila ya ba da umarni ga dakarun ƙasar da su ci gaba da kai farmaki a kan Tehran, yana mai cewa Iran ce ta fara karya yarjejeniyar.
Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra’ila ta yarda da tsagaita wuta, amma za ta kare kanta idan Iran ta sake kai mata hari.
Asali: Legit.ng