Ibrahim Yusuf
5427 articles published since 03 Afi 2024
5427 articles published since 03 Afi 2024
Gwamnatin jihar Filato ta kafa sababbin dokoki saboda hana kashe kashe a jihar. An hana kiwon dare da takkaita zirga zirga da babura da zirga zirgar shanu da dare.
Dan daba da aka fi sani da Abba Dujal ya mika wuya ga 'yan sandan jihar Kano. Dujal ya ce ya kashe mutane a Kano da Jigawa, ya sace babura da wayoyin jama'a.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai dawo APC saboda NNPP ta mutu murus a Najeriya. Ganduje ya ce masu shirin hadaka za su wargaje.
Majalisar sarakunan Arewa ta gudanar da taronta na bakwai a Maiduguri na jihar Borno. Taron ya mayar da hankali ne kan lamuran tsaro da suka addadi jama'a.
Majalisar wakilai ta kafa kwamiti mai mutane 21 domin lura da harkokin majalisar dokokin Rivers da aka dakatar. Kwamitin zai lura da aikin da shugaban riko ke yi.
Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun fara zawarcin Sanata Kawu Sumaila ya fita daga NNPP zuwa APC yayin da ake cigaba da samun sabani tsakanin shi da Kwankwaso.
Wata kungiyar matasa ta bayyana cewa za ta hada kan mutane miliyan 5 domin nuna jin dadin mulkin Bola Tinubu a jihar Abia tare da goyon bayan Sanata Orji Kalu.
Gwamnan jihar Filato ya yi zama da sojoji, 'yan sanda da shugabannin kananan hukumomi kan kashe kashe da ake fama da shi a jihar. Ya ce za su hana kai hare hare.
Kamfanonin da ke samar da wutar lantarki na Gencos sun bayyana cewa za su dakatar da aiki kan bashin Naira triliyan 4 da suke bin gwamnatin Najeriya.
Ibrahim Yusuf
Samu kari