‘Farashin Abinci Ya Zube Kasa Warwas a Najeriya Saboda Tsare Tsaren Tinubu’
- Fadar shugaban ƙasa ta ce farashin kayan abinci ya ragu sosai, inda ta bayyana cewa buhun shinkafa ya yi kasa sosai
- Bayo Onanuga ya ce hauhawar ajiyar kuɗaɗen waje da ƙarin jarin ƙasashen waje na nuna cewa sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu
- Duk da ikirarin gwamnati, har yanzu ’yan Najeriya na nuna damuwa kan tsadar rayuwa, yayin da farashin kayan abinci ya bambanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi magana game da tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu na bangaren tattalin arziki.
Ta bayyana cewa farashin muhimman kayan abinci, ciki har da shinkafa, ya ragu sosai, tare da zargin wasu ’yan jarida da yaɗa ikirarin ’yan adawa.

Source: Twitter
Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Ana samun ci gaba tattalin arziki
Onanuga ya ce tattalin arzikin Najeriya na samun gagarumin ci gaba duk da sukar ’yan adawa da ke cewa manufofin tattalin arzikin Tinubu sun gaza inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Ya kawo raguwar farashin shinkafa, ƙarin ajiyar kuɗaɗen waje da kuma bunƙasar jarin ƙasashen waje a matsayin hujjojin cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu na haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa, buhun shinkafa da a baya ake sayarwa har kan ₦120,000, yanzu ana samunsa a ƙasa da ₦50,000 a wasu kasuwanni.
Ya ce:
“A garinmu, yanzu ana sayar da buhun shinkafa kan ₦45,000.”
Mai magana da yawun shugaban ƙasa ya zargi masu gabatar da shirye-shiryen talabijin da ci gaba da yaɗa ra’ayin ’yan adawa cewa babu wani babban sauyi tun bayan da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023.
Haka kuma, ya soki masu shakkun alkaluman hauhawar farashin kayayyaki da gwamnati ke fitarwa, inda ya bukace su da su je kasuwanni domin tantance rahotannin raguwar farashin abinci.

Source: Twitter
Farashi ka iya bambanta daga kasuwa zuwa kasuwa
Onanuga ya jaddada cewa shugaban ƙasar ya aza tubalin bunƙasar tattalin arziki mai ƙarfi, kuma yana tsara hanyoyin da za su kai Najeriya ga samun ci gaba da wadata.
Sai dai ikirarin fadar shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da nuna damuwa kan tsadar rayuwa.
Tasirin farashin abinci ya bambanta daga kasuwa zuwa kasuwa da kuma tsakanin yankuna, don haka farashin shinkafar da ya ambata a garinsu ba lallai ne ya zama hakaa ko ina ba.
'Dalilin gwamnoni 33 na bin Tinubu' - Onanuga
A baya, an ji cewa hadimin shugaban kasa a Najeriya ya ce gwamnonin jihohi 33 ba za su yi kuskure ba wajen goyon bayan Tinubu.
Bayo Onanuga ya ce farashin kayan abinci ya ragu, ajiyar kuɗin ƙasashen waje ta ƙaru, sannan ’yan Najeriya sun fara amfani da katunan bankinsu ƙasashen waje.
Ya kuma ce masu zuba jari na ƙasashen waje sun dawo Najeriya, suna kawo kuɗaɗe da samar da ayyukan yi, duk da sukar da ake yi wa tattalin arzikin ƙasar.
Asali: Legit.ng

