Sojoji Sun Kashe Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Ceto Wanda Aka Sace a Kano

Sojoji Sun Kashe Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Ceto Wanda Aka Sace a Kano

  • Sojoji sun kashe mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da ceto Alhaji Kabiru Aliyu a dajin Falgore da ke Kano
  • An kwato Naira miliyan 10 da iyalan wanda aka sace suka biya a matsayin kudin fansa ga wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne
  • Sauran mambobin kungiyar sun tsere bayan samamen hadin gwiwar sojoji da 'yan sanda, DSS da mafarautan yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun ceto wani da aka sace tare da kwato kudin fansa na Naira miliyan 10 a wani samame da suka kai dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Samamen da dakarun Brigade ta 3 karkashin rundunar Operation MESA suka gudanar ya biyo bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a kauyen Fanyabo da ke dajin Falgore a ranar 11 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan kasuwa 2000 suka yi asara, an rasa rayuka a gobarar tankar mai a Edo.

An kashe masu garkuwa a Kano
An hallaka masu garkuwa da mutane a Kano
Source: Original

An sace mutum a hanyarsa ta dawowa

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Brigade ta 3, Major Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Asabar, ya ce an sace Kabiru ne da misalin tsakar dare lokacin da yake dawowa daga kasuwar Yandoka da ke jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce daga bisani masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansa da ke kauyen Yan Taburmi, shi ma a dajin Falgore, inda suka bukaci a biya kudin fansa domin sakin sa.

An kwato N10m na fansa

Bisa ga sanarwar, sojojin sun samu sahihan bayanan sirri kafin su shirya kwanton bauna tare da hadin gwiwar 'yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da mafarautan yankin.

Samamen ya yi sanadin kashe mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da samun nasarar ceto wanda aka sace. Sai dai sauran mambobin kungiyar sun tsere zuwa cikin dajin Falgore.

Kara karanta wannan

Yadda tawagar ofishin Ribadu suka ceto mata, miji da jaririyarsu da aka sace

Sanarwar ta kara da cewa binciken da aka gudanar a yankin bayan samamen ya kai ga gano Naira miliyan 10 da aka ce iyalan wanda aka sace sun biya a matsayin kudin fansa.

An mayar da kudin ga wanda aka ceto da iyalansa, a cewar sanarwar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar 17 ga watan Oktoba, 2026.

Sojoji sun yi gargadi

Kwamandan Brigade ta 3, Birgediya Janar Saka Jimoh, ya yaba wa dakarun saboda kaifin basira, kwarewa da jajircewa da suka nuna yayin gudanar da aikin.

Jimoh ya sake jaddada kudurin rundunar na ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka da kuma hana sake samun barazanar tsaro a yankin.

Ya kuma bukaci jama'a da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano.

Yadda kare ya addabi wasu a Kano

A bangare guda, akalla mutane 18 ne aka ruwaito cewa wani kare da ake zargin yana dauke da cutar hauka ya cije su a karamar hukumar Garko ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke dan babban Shehin Darika a Najeriya kan badakalar kudi

Bayan faruwar lamarin, Hukumar Tsaron Daji ta Najeriya (NFSS), reshen Garko, ta fara neman karen da wasu karnuka biyu da ake zargin sun kamu da cutar.

Wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar NFSS ta jihar Kano, CSF Usman Abdullahi Umar, ya sanya wa hannu, an ce ofishin hukumar na Garko ne ta bayyana rahoton faruwar lamarin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng