Musulmai Sun Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ya Rasu

Musulmai Sun Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ya Rasu

Gombe, Nigeria - Sheikh Saidu Imam, babban limamin Masallacin Juma’a na Shagon Goro da ke jihar Gombe a Arewa maso Gabashin Najeriya ya riga mu gidan gaskiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Babban limamim, wanda malami ne a kungiyar Izala reshen jihar Gombe ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Dan marigayin, Abdulhayyu Said Imam ya tabbatar da rasuwar mahaifin na su a wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2026.

Ya bayyana cewa za a yi jana'izar malamin da misafin karfe 1:00 na tsakar ranar yau Litinin a masallaci na I da ke Commercial Area a jihar Gombe.

"InnalilLahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya yi wa mahaifin mi rasuwa, Sa'idu Imam. Za a yi jana'iza da karfe 1:000 na rana a masallacin Juma'a na daya New Commercial Arewa, Gombe."

Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Oantami ya tabbatar da rasuwar malamin, inda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Sheykh Saidu Imam.

Kara karanta wannan

Ana batun cire sunayen wasu 'yan takara, shugaban jam'iyyar PDP ya yi murabus

A sakon da ya wallafa a Facebook, Sheikh Pantami ya ce:

"Mun yi babban rashi na ɗaya daga cikin fitattun malamanmu da masu ba mu tarbiyya, Sheikh Saidu Imam, babban limamin Masallacin Juma’a na Shagon Goro da ke Gombe.
"Muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalansa, musamman Dakta Abubakar Saidu Imam, da sauran ’yan uwansa, ɗalibansa, abokansa, maƙwabtansa da abokan hulɗarsa.

Pantami ya ce Marigayi Sheikh Saidu Imam mutum ne da ya yi fice wajen haɗa kan al’umma, wanzar da zaman lafiya da kuma tawali’u. Ya kasance masani sosai, mai fara’a, mai tsananin tawali’u kuma mai riƙon amana.

Ya ce kimanin makonni uku da suka gabata, ya kai masa ziyara tare da Alhaji Hussaini Ahmad Ganga (Ɗan Amar na Gombe), Alhaji Usman Gurama da Dakta Abubakar Saidu (Dakta Yagi), domin jajanta masa kan rashin lafiyar da yake fama da ita.

"Za mu yi matuƙar kewar zallar muryarsa mai daɗi yayin gabatar da huɗubar sallar Juma’a da kuma wa’azuzzukansa na mako-mako, musamman waɗanda suka shafi ranar Alƙiyama.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Mawakin addini a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

"Idanu suna zubar da hawaye, zuciya kuma tana cike da baƙin ciki, amma ba za mu faɗi komai ba sai abin da Ubangijinmu Ya yarda da shi. Hakika, Shaykh Saidu Imam, mun yi babban rashi sakamakon tafiyarka."

Daga karshe Pantami ya roki Allah Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus tare da iyayenmu da sauran masoyanmu da suka riga mu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262