Lokacin Tafiya Ya Yi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu Yana d Shekaru 71 a Duniya
- Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Delta, Dr. Emmanuel Eweta Uduaghan, ya rasu yana da shekaru 71 a duniya
- Marigayi Uduaghan ya rike kujerar gwamnan jihar Delta na tsawon wa’adi biyu, daga shekarar 2007 zuwa 2015
- Iyalan marigayin sun bayyana rasuwar Uduaghan a matsayin babban rashi ga iyalansa, Jihar Delta da Najeriya baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Delta, Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 71 da haihuwa a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa Uduaghan ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 19 ga Oktoba, kamar yadda wata sanarwa da iyalansa suka fitar, wadda Toju Anire Uduaghan ya sanya wa hannu, ta bayyana.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Delta ya mutu
Iyalansa sun sanar da rasuwarsa ne cikin wata sanarwa da jaridar Leaderdhip ta gani, inda suka bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.
Sanarwar ta bayyana tsohon gwamnan a matsayin dattijo mai daraja, wanda rayuwarsa da hidimar da ya yi wa jama’a suka shafi mutane da dama a faɗin jihar da ƙasar nan baki daya.
Iyalan tsohon gwamnan sun ƙara da cewa za su ci gaba da tunawa da shi da kuma kyawawan abubuwan da ya bari a baya.
Tarihin ayyukan tsohon gwamnan
Emmanuel Uduaghan ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan lafiya na Jihar Delta daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan ya zama sakataren gwamnatin jihar daga 2003 zuwa 2007, kafin ya zama gwamna a shekarar 2007.
Ya jagoranci jihar Delta na tsawon wa’adi biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, inda ya bar muƙamin a shekarar 2015 bayan shafe shekaru takwas yana mulki.
A cewar iyalansa, ya nuna jajircewa wajen bunƙasa rayuwar al’umma da samar da ababen more rayuwa a Jihar Delta a tsawon shekarun da ya yi yana hidimar jama’a.

Source: Original
Sun mika godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa rayuwar da ya ba shi da kuma hidimar da ya yi, tare da roƙon Allah Ya ba ’yan uwansa, abokansa, abokan hulɗarsa, tsoffin abokan aikinsa da sauran waɗanda ke alhinin rasuwarsa haƙurin jure wannan rashi.
A rahoton Daily Trust, sanarwar ta ce:
“Rasuwarsa babban rashi ne ga iyalanmu, al’ummar Jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.”
Haka kuma, iyalan sun roƙi Allah Ya sa mamacin ya huta lafiya, tare da bayyana cewa tunawa da shi za ta ci gaba da kasancewa a zukatan mutanen da ya taɓa rayuwarsu a lokacin da yake raye.
Dattijon kasa, Ralph Obioha ya rasu
Kun ji cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa National Democratic Coalition (NADECO), Cif Ralph Obioha, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 80.
Iyalansa sun bayyana shi a matsayin uba, miji, ɗan’uwa, kaka da aboki mai matuƙar ƙauna, sun ce ya rasu ne ranar 3 ga Oktoba, 2026
Asali: Legit.ng

