Abin da Ya Fi Firgita Kashim Shettima kan Zaben 2027 Fiye da Atiku da Obi

Abin da Ya Fi Firgita Kashim Shettima kan Zaben 2027 Fiye da Atiku da Obi

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana abin da yafi ba shi tsoro fiye da Atiku Abubakar da Peter Obi gabanin zaɓen 2027
  • Shettima ya buƙaci ’yan APC a Arewa su haɗa kai, su goyi bayan shugabanninsu da Bola Tinubu
  • Ya kare nasarorin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa ajiyar kuɗin waje ta Najeriya ta kai dala biliyan 58.9, tare da yi wa yan Arewa alkawari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana damuwa game da tsoron rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar APC.

Kashim Shettima ya matsalar a jam'iyya mai mulki tana ba damuwa fiye da tsoron ’yan adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kashim Shettima ya shawarci yan APC
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

Shettima ya kaddamar da ofishin kamfen Tinubu

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ƙaddamar da babban ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yan takarar gwamnan jam'iyyar adawa sun fadi wanda za su yi a zaben shugaban kasa

Kungiyar wacce ta yi hadakar ƙungiyoyin Arewa ce da ke goyon bayan tikitin Bola Tinubu da Kashim Shettima, tare da buɗe tsarin gudanar da yaƙin neman zaɓenta.

Ya ce:

“A gaskiya, ba na tsoron jam’iyyar PDP. Ba na tsoron Peter Obi da tasirinsa ya ragu, amma na fi tsoron saɓani da rikice-rikicen cikin gida a iyalinmu. Idan muka haɗa kai a matsayin al’umma da iyali, za mu yi nasara.”

Ya gargaɗi shugabannin Arewa da kada su biɗi nasarar zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar raunana gwamnoninsu a zaɓen gwamna.

Kashim Shettima ya yi magana kan tasirin Atiku da Obi
Jagororin adawa a Najeriya, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Mr Peter Obi.
Source: UGC

Shettima ya tunatar da yan APC kusancin zabe

Shettima ya shaida wa mahalarta taron cewa zaɓen ya kusa inda ya ce nan da kwanaki 100 yan kasar za su sake fita zabe.

Ya ce:

“Babu wata fa’ida a goyi bayan zaɓen shugaban ƙasa, sannan a yi ƙoƙarin kawo cikas ga gwamna a zaɓen gwamna. A gaskiya, hakan ba zai yi wa tsarin siyasa daɗi ba.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

"Mu haɗa kai wajen tallafa wa gwamnoninmu. Mu goyi bayan ’yan majalisun tarayya. Mu kuma mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ganin mun samu nasara a zaɓe mai zuwa.
“A cikin kwanaki ƙasa da 100, ’yan Najeriya za su sake fita zaɓe. Dimokuraɗiyya na buƙatar mu sake neman amincewarsu cikin tawali’u game da ayyukan da suka rage, tare da yakinin kan manufar da muka zaɓa.”

Dangane da Atiku Abubakar, Shettima ya buƙaci ’yan jam’iyyar su fuskance shi cikin mutunci, cewar Punch.

Ya bayyana cewa APC tana da isasshen tsarin jam’iyya da zai ba ta damar fafatawa a kowace rumfar zaɓe.

Ya ce:

“Ku je ku yi aikinku. Ku je ku kayar da Baba Atiku. Ku kayar da shi cikin mutunci.”

Shettima: Kwankwaso ya ba Obi kariya

An ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso, ya soki mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, kan kiran Peter Obi ƙwararre wajen amfani da ƙididdiga marasa tushe.

Kwankwaso ya ce Obi ya san harkar ƙididdiga sosai, kuma yawancin alkaluman da yake gabatarwa suna da inganci idan aka bincika su.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa kowa na iya yin kuskure, amma bai yarda da kalaman Shettima kan ɗan takarar shugaban ƙasarsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.