Ahmad Yusuf
11634 articles published since 01 Mar 2021
11634 articles published since 01 Mar 2021
Har yanzun ƴaƴan APC a Arewa ta Tsakiya ba su hakura da kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa ba, wata kungiya ta fara neman waɗanda za su mara mata baya.
Mai fafutuka kare hakkin ɗan adam, Deji Adeyanju ya bayyana sunayen ministocin da yake ganin sun cancanci jinjina da kuma masu zaman dumama kujera.
Gwamnatin tarayya ta kafe kan ƙarin kudin wutar da ta wa ƴan Band A, amma ƴan kwadago sun ce ba za ta saɓu ba, ya zama dole a soke wannan karin a Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce a shirya yake ya marawa Obi baya matuƙar PDP ta amince za ta ba shi tikitin takara a zaɓen 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna alamun bai hakura da neman mulkin Najeriya ba, ya ce wuƙa da nama na hannun mambobin PDP.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci ƴan uwa da abokanan arziki su taimakawa waɗanda harin masallaci ya shafa a jihar.
Wata kungiyar magoya bayan APC ta jaddada cewa duk wani ƙawance da haɗa kai da ƴan siyasa ke shirin yi, ba za su iya kawar da Tinubu ba a babban zaɓen 2027.
Gwamna Seyi Makinde ya amince da ɗaukar malaman makaranta 7,000 da ma'aikata 100 a makarantun naƙasassu domin ingantar harkar neman ilimi a jihar Oyo.
Wani ɗan rikici ya faru tsakanin jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya DSS da wasu ma'aikata a zauren majalisar tarayya da ke Abuja, tuni dai an shawo kan lamarin.
Ahmad Yusuf
Samu kari