'Yan Kwadago Sun Ƙara Daukar Zafi, Sun Ba Tinubu Wa'aɗi Ya Janye Ƙarin Kuɗin Wuta

'Yan Kwadago Sun Ƙara Daukar Zafi, Sun Ba Tinubu Wa'aɗi Ya Janye Ƙarin Kuɗin Wuta

  • NLC da TUC sun bai wa gwamnati wa'adin kwanaki 11 ta janye ƙarin kuɗin wutar lantarkin da ta yi wa ƴan rukunin Band A
  • Ƙungiyoyin sun jaddada cewa ba gudu ba ja da baya ba za su lamurci ƙarin ba a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama da kuncin rayuwa
  • Tun farko ƴan kwadago sun gudanar da zanga-zanga a ofisoshin NERC na faɗin Najeriya domin nuna adawarsu da ƙarin kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC sun bai wa gwamnatin tarayya wa'adin daga nan zuwa karshen watan Mayu ta soke ƙarin kuɗin wutar lantarki.

Ƴan kwadagon sun ɗauki wannan matakin na gindaya wa gwamnati wa'adi ne a wurin taron majalisar zartarwa (NEC) na haɗin guiwa da suka gudanar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a birnin tarayya Abuja, sun gamu da matsala

Shugabannin NLC da TUC.
NLC da TUC sun bai wa gwamnatin Tinubu wa'adi kan karin kudin wuta Hoto: @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Kamar yadda Punch ta ruwaito, ƴan kwadagon sun kuma nanata bukatar a soke wannan ƙarin kuɗin da aka ƙaƙabawa ƴan rukunin Band A.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin sun kara jaddada matsayarsu na yin Allah-wadai da ƙarin kuɗin wutar da gwamnatin tarayya ta yi ba tare da duba halin matsin tattalin arziki da mutane ke ciki ba.

Wutar lantarki: NLC, TUC sun ɗauki zafi

A sanarwar da aka fitar bayan taron, NEC ta ce:

"NEC ta sake yin Allah wadai da karin kudin wutar lantarki da hukumomi suka yi. An ɗauki matakin ba tare da la’akari da matsin tattalin arziki da talakawa ke fuskanta da kuma tanadin doka ba.
"Muna ƙara nanata bukatar cewa a gaggauta janye ƙarin kuɗin wutar da aka yi wa rukunin Band A domin rage raɗaɗin da ma'aikata da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin maƙudan tiriliyoyin kuɗi da ake bin Najeriya

"Saboda haka mun ba wa hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa da gwamnatin tarayya daga nan zuwa ranar 31 ga watan Mayu, su janye wannan ƙarin."

Idan ba ku manta ba a makon jiya ne ƴan kwadago suka mamaye ofisoshin hukumar NERC na faɗin ƙasar nan saboda ƙarin kuɗin wuta, The Nation ta ruwaito.

Gwamnati za ta sake zama da NLC

A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya za ta sake zama da kungiyoyin kasar nan kan batun mafi karancin albashi da zummar cimma matsaya.

A Larabar da ta gabata ne kungiyar kwadago ta NLC ta fice daga taron da kwamitin duba kan mafi karancin ta kira saboda rashin amincewa da matakin da su ka dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel