Gwamnan PDP Ya Shirya Zai Tsamo Sama da Mutane 7,000 Daga Ƙangin Rashin Aikin Yi

Gwamnan PDP Ya Shirya Zai Tsamo Sama da Mutane 7,000 Daga Ƙangin Rashin Aikin Yi

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da ɗaukar sababbin malaman firamare 7000 da ma'aikatan makarantun nakasassu
  • Shugaban hukumar hula da ilimi a matakin farko na jihar Oyo, Dakta Adeniran ne ya bayyana haka ranar Jumu'a a Ibadan
  • Ya ce wannan na ɗaya daga cikin alƙawurran da mai girma gwamnan ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa kuma zai cika nan kusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo karkashin jagoranci Gwamna Seyi Makinde ta ce za ta ɗauki sababbin malamai 7,000 a faɗin kananan hukumomin jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa malaman da za ta ɗauka za su yi aiki ne a makarantun firamare domin inganta harkar koyo da koyarwa a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamnatin jihar Oyo ta shirya ɗaukar sababbin malamai 7,000
Asali: Twitter

Shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko ta jihar Oyo (OYOSUBEB), Dakta Nureni Aderemi Adeniran ne ya sanar da haka a wata hira da ƴan jarida a Ibadan ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde zai ɗauki ƙarin ma'aikata

Gwamnatin jihar ta kuma ce za a dauki ma’aikata dari (100) aiki a bangaren masu bukata ta musamman a Oyo, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Da yake jawabi a yayin taron manema labarai, Dakta Adeniran ya ce tuni suka fara shirin daukar sababbin malaman domin cika alkawarin Gwamna Seyi Makinde.

"Gwamna Seyi Makinde ya amince da daukar malamai 7,000 a makarantun firamare na gwamnati. Bugu da kari, ya amince da daukar ma’aikata 100 masu ba da kulawa a makarantun naƙasassu.
"Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnan na cika alƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe da kuma cika muradin al'ummar jihar Oyo."

Kara karanta wannan

"Ko a jikina," Ministan Tinubu ya maida martani kan abubuwan da ke faruwa a Rivers

- Dakta Adeniran.

Ya kuma yi kira ga masu neman a ɗauke su wannna aiki da su kula kada su fada hannun ‘yan damfara, kuma su yi hattara da masu ƴan zamba, rahoton Pulse.

Dokta Adeniran ya jaddada cewa hukumar ba ta nada kowa a matsayin wakili ba, inda ya kara da cewa a yanzu sun fara aikin share fage ne a tsarin daukar ma’aikatan.

PDP ta lashe zaɓen ciyamomi a Oyo

A wani rahoton kuma Jam'iyya mai mulki ta PDP a jihar Oyo ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 33 na jihar.

Hukumar zabe ta jihar Oyo (OYSIEC) ce ta sanar da sakamakon zaben ciyamomin jihar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel