Goodluck Jonathan Ya Tsoma Baki Kan Rigimar Ministan Tinubu da Gwamnan PDP

Goodluck Jonathan Ya Tsoma Baki Kan Rigimar Ministan Tinubu da Gwamnan PDP

  • Goodluck Jonathan ya nuna matuƙar damuwa kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Nyesom Wike da magajinsa, Siminalayi Fubara a jihar Ribas
  • Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci a kawo ƙarshen wannan rikici yayin da alaƙa ke ƙara tsami tsakanin manyan jiga-jigan biyu
  • Dokta Jonathan ya yi kira ga Wike da Fubara su yayyafa wa wutar rikicin ruwan sanyi domin abin da ke faruwa tsakaninsu ya daƙile ci gaban jihar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci a sasanta rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Ribas domin dawo da zaman lafiya.

Jonathan ya kuma roƙi Gwamna Siminalayi Fubara da ministan Abuja, Nyesom Wike su kawo ƙarshen wannan lamari kuma su haɗa kai su yi aiki tare.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

Jonathan ya nemi sasanta Wike da Fubara.
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya bukaci Wike da Fubara su binne saɓanin da ke tsakanin su Hoto: Goodluck Jonathan, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Rikicin siyasa da Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu a wurin kaddamar da titin Trans-Kalabari a jihar Ribas, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa a halin yanzu fada tsakanin gwamnoni da magabatan su ya zama ruwan dare a kasar nan, in da ya ce irin haka na kawo wa jihohi koma baya, rahoton The Nation.

Jonathan ya kawo mafita a rikicin Rivers

"Ya zama dole gwamnoni masu barin gado da gwamnonin da ke kan karagar mulki su yi aiki tare domin sauke nauyin jama’a, kuma hakan yana da matukar muhimmanci.
"Dangane da jihar Ribas kuwa, dole ne Minista Nyesom Wike da Gwamna Sim Fubara su hada kai domin ci gaban ƙasa da al’ummar Jihar Ribas. Rigima ba za ta amfani kowa ba.

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

"Ina rokon ku dawo inuwa ɗaya idan kuna ƙaunar al'ummar jihar Ribas, ni dai ina ɓangaren shugabanni da masu fatan alheri waɗanda ke ta kiraye-kirayen a sasanta rikicin jihar nan.
"Muna kira gare su (Wike da Fubara) su rungumi juna, ba a tafi da hannu ɗaya dole sai an haɗa hannu biyu. Muna son mu ga sun koma inuwa ɗaya suna aiki tare."

- Goodluck Jonathan

Wike da Fubara sun dade suna takun saka, har sai da shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani don warware matsalar amma abun ya ƙi ci ya ƙi cinyewa har kawo yanzu.

Fubara ya soki shekara 8 na Wike

A wani rahoton kuma Gwamna jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce ayyukan da ya gudanar a jihar ya fi shekaru takwas na gwamnatin da ta shude.

Fubara ya na magana ne kan gwamnan mai gidansa, Nyesom Wike inda ya ce ya kawo ayyukan alheri a cikin shekara daya kacal da ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262