Kwankwaso da Peter Obi Za Su Haɗa Kai da Atiku a 2027, Jigon PDP Ya Yi Bayani

Kwankwaso da Peter Obi Za Su Haɗa Kai da Atiku a 2027, Jigon PDP Ya Yi Bayani

  • Jigon jam'iyyar PDP, Dare Glintstone Akinniyi, ya bayyana muhimmacin dawowar Peter Obi babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa
  • Akinniyi, kakakin ƙungiyar matasan PDP na ƙasa ya ce sauya sheƙar Obi zuwa LP ya taimakawa APC, inda ya ce ya kamata ya canza tunani kafin 2027
  • Da yake hira da Legit.ng, jigon PDP ya nuna cewa lokaci ya yi da Kwankwaso, Peter Obi da kuma Atiku Abubakar za su haɗa kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Mai magana da yawun ƙungiyar matasan jam'iyyar PDP na ƙasa, Dare Glintstone Akinniyi, ya roƙi Peter Obi, ɗan takarar LP a zaɓen 2023 ya haƙura ya dawo PDP.

Mista Akinniyi ya bayyana cewa yana da muhimmanci Obi ya farfaɗo da alaƙarsa da Atiku kana ya sake komawa jam'iyyar PDP gabannin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen Atiku ya faɗi lokacin da Peter Obi zai iya hawa mulkin Najeriya

Kwankwaso da Obi da Atiku.
Jigon PDP ya ce lokaci ya yi manyan ƴan adawa zasu kaɗa kansu Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Shugaban matasan ya yi wannan jawabin ne yayin hira da Legit.ng ta wayar tarho ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi da Kwankwaso suna da muhimmanci

Bayan Obi, Akinniyi ya kuma roki Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da sauran manya-manyan ƴan adawa su haɗa kai wuri ɗaya su marawa Atiku baya.

Ya ce lokaci ya yi da ƴan adawa za su dunƙule wuri ɗaya su goyi bayan Atiku domin kawo ƙarshen mulkin APC a 2027 ba don komai ba sai don kishin talakawa.

Obi zai dawo wajen Atiku a PDP?

Idan baku manta ba, Peter Obi ya gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa. Atiku da wasu manyan ƙusoshin PDP a Abuja ranar 14 ga watan Mayu, 2024.

Obi ya bayyana cewa ya kai wa manyan ƴan siyasar ziyara ne domin tattauna halin da ƙasar nan ke ciki da kuma yadda za a ceto ƴan Najeriya daga wahala.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisa ya ba Ganduje mafita wajen warware rikicin jam'iyyar APC

Yadda PDP zata kawar da APC

Da yake mayar da martani kan haka, Mista Akinniyi ya ce:

"A yanzu, Obi ba shi da zaɓin da ya wuce ya juyo zuwa PDP, sauya sheƙar da ya yi zuwa Labour Party ya taimakawa APC ne kawai."
"Yana da muhimmanci mu haɗa Obi da sauran ƴan adawa ciki har da Rabiu Kwankwaso na NNPP, su dawo PDP kana su marawa jagoran adawa, Atiku baya gabanin 2027.
"Idan har dagaske saboda talakawa suke yi to ya kamata su haɗa kai wuri ɗaya domin kawar da gwamnatin APC ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu."

Bwala ya takali Peter Obi

A wani rahoton kuma jigon jam'iyyar PDP, Daniel Bwala, ya tsokani ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party a zaɓen 2023, Mista Peter Obi.

Duk da raɗe-raɗin PDP ka iya haɗa maja da LP, Bwala ya ce a zaɓen 2039 ne kaɗai za a iya cewa Obi na da damar zama shugaban ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel