Gwmnatin Buhari ta shirya kwato £200m da aka sace aka boye a Amurka

Gwmnatin Buhari ta shirya kwato £200m da aka sace aka boye a Amurka

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana yunkurinta na kwato wasu kudaden da aka sace su mallakin kasar
  • Wannan na zuwa ne yayin da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya ke tattaunawa a wani taro a Amurka
  • Ya bayyana cewa, gwamnati na shirya wasu hanyoyi don tabbatar da kwato kudaden kasar nan cikin sauki

New York, US - Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kwato fam miliyan 200 da aka sace aka boye a Amurka, yayin da gwamnatin ke shirin fara kwato kadarori mallakin kasar.

Yunkurin ya fito ne ta bakin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami wanda ke magana a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York ta kasar Amurka.

Gwmnatin Buhari ta shirya kwato £200m da aka sace aka boye a Amurka
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami | Hoto: gaurdian.ng
Asali: UGC

Channels Tv ta tattaro cewa, da yake magana kan yaki da cin hanci da rashawa da kwararar kudade a kasar, Malami ya ce:

Kara karanta wannan

Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida

"Muna duba yiwuwar dawo da fam miliyan 200 da wasu kari amma to, hakan ba yana nufin babu wasu kadarorin da ake alaka da su ba, dangane da sauran kasashen duniya da suka hada da Ireland.
"Muna bibiyar kadarori da yawa a duk fadin duniya sannan muna da niyyar shirya karin tarurrukan da suka shafi dawo da kudade a Burtaniya wanda ke da alaka da wasu mutane."

AGF ya ce ba zai so ya kara bayyana dabarun da gwamnatin tarayya za ta bi wajen dawo da kudade ba, amma ya lura cewa:

“Gwamnati na kokarin tattara karfin duniya da ke da alaka da matakai da hanyoyi, dangane da saukake lamurra ga kasashe wajen dawo da kadarori cikin sauki."

Ya kara da cewa gwamnati ta himmatu ga yakin da take yi da cin hanci da rashawa kuma ta hanyar fadada shimfida tarkon ta ga wadanda ke boye da kudaden da aka sace ko aka tsallakar.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

'Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Ya fadi haka ne lokacin da Babban Sakataren PIC ya bayyana a kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

A wani labarin, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar bayyana suna da kunyatar da masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci, TheCable ta ruwaito.

Adesina ya fadi haka ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels.

A makon da ya gabata, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanya 'yan Najeriya shida cikin jerin 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel