'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

  • 'Yan sanda a kasar New Zealand su kame wasu mutane biyu dake kokarin shigo da kaji daga wata jiha
  • Wasu yankuna a kasar na fama da annobar Korona, wannan yasa aka hana kasuwancin abubuwa daban-daban
  • 'Yan sanda sun kame mutanen da soyayyun kaji masu yawa yayin da ake kokarin tsallakawa dasu

New Zealand - 'Yan sandan New Zealand sun kama wasu mutane biyu da ke kokarin shigo da mota da ke cike da soyayyun kaji zuwa Auckland, The Punch ta ruwaito.

Auckland, birni mafi girma a kasar, yana cikin tsauraran ka'idojin takunkumi na Korona tun tsakiyar watan Agusta, ba tare da an ba kowa izinin shiga ko barin yankin ba.

Duk kasuwancin da ba su da mahimmanci, wanda ya hada da wuraren cin abinci na kan titi, an rufe su a Auckland. Sai dai, sauran yankunan New Zealand na da karancin ka'idoji tare da kusan dukkanin nau'ikan kasuwanci a bude.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

'Yan sanda sun cafke mota makare da soyayyun kaji da aka yi fasa-kwabrinsu
Soyayyun Kaji | Hoto: cookpad.com
Asali: UGC

'Yan sanda sun ce jami'an da ke sintiri kan hanyoyin da ke kusa da kan iyaka sun lura da motar "abin zargi" tana tafiya a kan lalatacciyar hanyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da hango motar 'yan sanda, motar ta juya baya ta gudu daga yankin, in ji kakakin 'yan sandan a cikin wata sanarwa.

Daga baya motar ta ja da baya kuma 'yan sanda sun tabbatar da cewa sun taho ne daga garin Hamilton da ke kusa inda suke kokarin shiga Auckland.

An bincika motar kuma 'yan sanda sun gano fiye da dalar New Zealand 100,000 (kimanin dala 70,207 na Amurka), holokon buhunna, da "adadi mai yawa" na soyayyun kaji.

'Yan sanda sun ce za su gurfanar da mutane biyu masu shekaru 23 da 30 da suka kama a gaban kuliya.

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Ma’aikata bakwai na Ma’aikatan Kiwon Lafiya na Kananan Hukumomin Kwami da Billiri a Jihar Gombe a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda saboda karkatar da 5,450 gidajen sauro masu magani (ITNs) da ake rabawa kyauta a al'ummomin su.

Gwamnatin jihar, tare da tallafi daga Asusun Duniya, Catholic Relief Serive da Shirin kawar da zazzabin cizon sauro sune masu tallafawa wajen rarraba gidajen sauron kyauta, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya a jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya fadawa wani taron manema labarai a Gombe ranar Asabar cewa an cafke wadanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba.

Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

A wani labarin, rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ta cafke wani mutumi ɗan kimanin shekara 45, Olaoluwa Jimoh, da zargin ɗirkawa ɗiyarsa ciki a yankin Ode-Remo, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin rundunar yan sandan Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar.

Wani sashin jawabin yace: "Hukumar yan sanda ta damƙe Jimoh a ranar 16 ga watan Satumba bisa zargin ɗirkawa yarsa da ya haifa ciki, yar kimanin shekara 19."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel