Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta bayyana cewa, a halin yanzu ba ta da sha'awar ambatan sunayen masu aikata laifuka
  • A cewarta, ba kunyata su ne a gabanta ba, abin da ta sanya a gaba shi ne tabbatar da hukunta masu daukar nauyin ta'addanci
  • Wannan na zuwa ne daga bakin mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina a cikin wata hira da aka yi dashi

Abuja - Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar bayyana suna da kunyatar da masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci, TheCable ta ruwaito.

Adesina ya fadi haka ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

A makon da ya gabata, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanya 'yan Najeriya shida cikin jerin 'yan ta'adda.

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da aka tambaye shi ko shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi tsokaci kan batun ta’addanci a zauren Majalisar Dinkin Duniya da mutum shida da aka kama, Adesina ya ce gwamnatin tarayya za ta fi mayar da hankali ne kan gurfanar da wadanda ake zargi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ambatan suna da kunyatarwa ba za su zama wani dalili ba. Maimakon haka, gabatar da masu laifi a gaban shari'a zai fi kyau. Najeriya ba ta da sha’awar ambatan suna da kunyatar da kowa. Maimakon haka, tana son gurfanar da su ne a gaban kuliya.

“Za ku ga Hadaddiyar Daular Larabawa ta ambaci wasu sunaye, kuma babban lauyan tarayya ya mayar da martani kan wannan lamarin, yana mai cewa a kan lokaci, duk wadannan mutanen za su shafe kwanaki a kotu.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

"Ka tabbatar da cewa za a gurfanar da mutanen nan gaban shari'a kuma adalci zai tabbata."

Ana ci gaba da bincike kan masu daukar nauyin ta'addanci

Mai magana da yawun shugaban ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a fadin hukumomin tsaro daban-daban kan masu daukar nauyin ta'addanci, kuma za a gabatar da shaidu don gurfanar da su.

Ya kara da cewa:

“Ba za ku kai mutane gaban kotu ba ba tare da bincike ba. Ina tsammanin hatta shugaban EFCC, Bawa, yayi magana akai kwanan nan. Ana gudanar da bincike a matakai daban-daban.
“Zai kasance a matakin EFCC; zai kasance a matakin Hukumar Leken Asiri ta Kasa. Hukumomin tsaro daban-daban za su yi aiki a kai ta yadda a lokacin da wadancan mutanen za su bayyana a gaban kotu, za a sami abin da lauyoyi ke kira karar prima facie a kansu.”

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi na karfafa fashi da makami a arewa, Kungiyar CAN ta yi zargi

A wani labarin, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel