Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila

Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya hana yin aikin wutar Mambila wanda shekaru 40 kenan da ake maganar sa
  • Hadimin shugaban kasan Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai
  • A cewar Shehu, rigima ce ta barke tsakanin dan kwangilar da kuma gwamnati, hakan ya hana banki ba shi bashi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana kwararan dalilan da suka janyo aikin wutar lantarki na Mambila da ke jihar Taraba ya kasa tabbata tsawon lokaci ba a kammala ba.

Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, har wakilin BBC da kansa ya je wurin da aka bayar don yin tashar wutar lantarkin amma ya ga ba a fara yin aikin ba.

Kara karanta wannan

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Garba Shehu ya bayyana kwararan dalilan da suka dakatar da aikin

BBC ta samu nasarar tattaunawa da mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu inda ya bayyana dalilin da suka sa aikin bai tabbata ba.

Garba Shehu: Saɓani tsakanin gwamnati da ɗan kwangila ne ya hana aikin wutar Mambila
Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu: Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A cewar Garba Shehu:

“Kudin da aka kididdiga za su isa a kammala aikin gabadaya sun kai sama da $4,000,000 wanda aka tsara cewa bashi za a amsa a wurin wani banki dake kasar China.”

Shehu ya ce dan kwangilar ya kai karar gwamnatin Najeriya, hakan ya dakatar da aikin

Saidai kamar yadda BBC ta ruwaito, Shehu ya ce wata rigima ce ta barke tsakanin gwamnatin Najeriya da dan kwangilar daga nan bankin ya dakatar da bayar da bashin.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Shehu ya bayyana cewa:

“Wani dan kasuwa Leno Adesanya ya yi ikirarin cewa gwamnati ta ba shi kwangilar kawo ma’aikatan da za su yi aikin tashar wutar Mambila.”
“Sai dai da aka bincika an gano cewa ba a gabatar da kwangilar zuwa ofishin tantance kwangiloli ba don amincewa da ita.”
“Sakamakon haka ne dan kwangilar ya maka gwamnatin Najeriya kara har wurin kwamitin daidaito na ‘yan kasuwa dake kasar Paris inda ya bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shi $200,000,000 sannan ya saki kwangilar, sakamakon haka ya janyo China ta dakatar da bayar da bashin.”

Shehu ya ce aikin zai tabbata ne da zarar dan kwangilar ya janye karar da ya kai gwamnati.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel