Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida
- Shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida
- Kamar yadda aka gano, hukumar ta gurfanar da Nadabo Energy da shugabanta sakamakon wata harkallar N1.4 biliyan ta mai
- Bawa ya je gaban babbar kotun da ke zama a Ikeja ne saboda shi ya binciki lamarin yayin da ya ke jami'in hukumar
Ikeja, Lagos - Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya bayyana gaban Mai shari'a Sedoton Ogunsanya na babbar kotun Ikeja da ke jihar Legas a ranar Talata.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayyana ne domin bada shaida a matsayinsa na babbar shaidar masu kara a wata harkallar mai da aka waskar da kudi har naira biliyan 1.4.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Nadabo Energy da shugabanta, Abubakar Peters, kan zarginsu da karbe kudi har biliyan 1.4 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin mai tare da samun wasu takardun bogi.
Bawa ya binciki lamarin yayin da ya ke matsayin jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, ana zargin masu kare kansu da kara yawan man fetur din da suke samarwa gwamnatin tarayya zuwa tan maitan 14,000.
'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa
A wani labari na daban, Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya, ya ce 'yan ta'addan ISWAP sun fara gagarumin gangamin diban jama'a domin zama mambobinsu.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, rundunar sojin ta kaddamar da hare-hare kan miyagun 'yan ta'addan karkashin Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabasa ta kasar nan.
Daruruwan 'yan ta'adda da suka hada da manyan kwamandojinsu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a makonni kalilan da suka gabata.
Asali: Legit.ng