Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna

Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna

  • PDP ta caccaki karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, saboda kare Gwamna Matawalle wanda ya koma APC
  • Jam’iyyar adawar ta nace cewa sai Matawalle ya bar kujerar gwamnan domin mataimakinsa ya dare, inda ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Jam’iyyar adawar ta caccaki Keyamo saboda ikirarin da ya yi cewa ba za ta iya samun kotu ta kori Matawalle daga mukaminsa ba

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce tana nan kan matsayinta na cewa sai an rantsar da mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau a matsayin gwamnan jihar.

A cewar jam'iyyar adawar, gwamna Bello Matawalle ya rasa damar zama a kujerar a daidai lokacin da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abokan ango sun rikirkita aurensa, suna ta jifan mutane da bandir-bandir din kudi a cikin wani bidiyo

Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna
PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara ya maye gurbin Matawalle Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa PDP ta sake jaddada matsayinta game da rikicin na Zamfara a cikin wata sanarwa daga kakakinta, Kola Ologbondiyan.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

Matawalle: PDP ta caccaki Keyamo, ta nemi ya yi murabus

PDP ta maka Matawalle a babbar kotun tarayya da ke Abuja, tana neman a kore shi.

Amma, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo (SAN), ya ce jam'iyyar adawar ba za ta iya samun nasara ba a hukuncin kotun.

Da take mayar da martani, PDP ta far wa ministan, tana mai cewa ra’ayinsa na doka akwai rashin azanci.

Jam’iyyar ta kara da rokon Keyamo da ya yi murabus ya shiga kungiyar lauyoyin Gwamna Matawalle idan yana da sha’awar kare shi, jaridar Leadership ta ruwaito.

Jam’iyyun siyasa ne ke cin zabe a Najeriya, ba ‘yan takara ba - PDP

PDP ta ci gaba da jayayya cewa Najeriya na gudanar da tsarin jam’iyya ne, inda ta kara da cewa ‘yan takarar suna aiki ne kawai a matsayin wakilan jam’iyyunsu.

KU KARANTA KUMA: Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Da take bayyana hukuncin kotun koli kan Faleke da INEC, jam'iyyar adawar ta yi ikirarin cewa ita ke da mallakin kuri'un da Matallawe ya hau kan kujerar gwamnan jihar Zamfara da shi.

Sanarwar ta kara da cewa ba za a mikawa APC kuri'un ba.

Kotu ta sanar da ranan sauraran karar da PDP ta shigar kan sauya shekar gwamna Matwalle

A gefe guda, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin ta sanar da 16 ga watan Yuli don sauraron karar da ke kalubalantar sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya yi zuwa Jam’iyyar APC, Daily Trust ta ruwaito.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya sanya ranar ne bayan ya saurari karar da lauyan masu shigar da kara, Kanu Agabi (SAN) ya shigar.

Mai shari'a Ekwo ya amince da rokon sannan ya dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya kafa wa PDP hujja da shari'ar Atiku bayan ta fara shirin tsige Matawalle a kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel