Abokan ango sun rikirkita aurensa, suna ta jifan mutane da bandir-bandir din kudi a cikin wani bidiyo
- Bidiyon taron wani aure da aka yi kwanan nan a jihar Imo ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya
- A cikin bidiyon wanda ya shahara, abokan angon sun rikirkita abubuwa yayin da suka dunga ruwan kudi tare da jifan bakin da suka hallara da kudaden
- Wasu manyan yara da aka ce abokan ango ne sun ta jefa bandir din kudade a jeji
Abokan wani mutumi sun haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya sakamakon irin barin kudin da suka yi a wajen bikin aurensa.
Bidiyon bikin wanda aka gudanar a karamar hukumar Orlu da ke jihar Imo ya nuno manyan yara suna yiwa ma’auratan ruwan kudi.
KU KARANTA KUMA: An yi aure a Asabar, Ma’aurata sun yi hadari a Talata, za a birne Miji a ranar Laraba
A bidiyon na Instagram wanda shafin @instablog9ja ya wallafa, abokan angon sun juya wurin baki yayin da suka dunga jifansu da bandir bandir din kudade.
Wasu daga ciki sun je wani daji da ke kusa inda wasu yan tsirarun mutane suka bi su yayin da suka dunga jefa masu kudade suma.
An yi cece-kuce a kan bidiyon
@loveli_leo ya ce:
“Me yasa suka jefa kudi a jeji????? Shin wannan ne sabon yayin????”
@kemmykush_imo ya rubuta:
“Yawan fina-finan Kanayo o kanayo da sauransu na damuna..Ina kallon wannan da tashin sauti.”
@gfreezle ya yi martani:
“Jeji dole dai sai ka wahala kafin ka samu wannan kudin, hatta kudin kyauta a jeji za ka dauke shi.”
@topmqn_tech ya ce:
“Ina taya ma’auratan murna, Allah ya kara nasara!!!"
“Hakazalika, kai da ni da muke karanta wannan, abun farin ciki zai zamo namu a karshen shekarar.”
KU KARANTA KUMA: Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu
@thegriiimreaper ya ce:
“Wasu daga cikin wadannan idan kannensu suka tambaye su kudin makaranta za su ce basu da shi.”
Manyan yara sun yi ruwan kudi a wajen wani liyafar biki da aka yi a Benin
A wani labarin, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu manyan yara suna jefa kudi a sama a wajen wani bikin aure a Benin, babban birnin jihar Edo.
Yaran sun fito da damin kudi masu yawa inda suka dunga jefa su a iska sannan kuma an gano baƙi da suka hallara suna ta dibar rabonsu.
A bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram ta @instablog9ja, an ga yaran ma a filin suna ta yi wa wasu baƙi liki yayin da kudade suka cika filin.
Asali: Legit.ng