Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ra'ayinsa game da batun mulkin karba-karba a cikin jam'iyyar All Progressive Congress
  • Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya ce babu wanda ke da ikon yanke irin wannan shawarar ga jam’iyya mai mulki
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki na gudanar da rajistar mambobin don kafa gidauniyar da za ta zarce gwamnatinsa

A yayin da ake tsaka da neman a mika tikitin takarar Shugaban kasa ga yankin kudu a 2023, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shawarar ta na ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Punch ta ambaci wata hira da yayi da gidan talbijin na Arise wanda aka watsa a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya ce mutum daya ba zai iya zartar da hukunci kan mulkin karba-karba ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023
Shugaba Buhari ya ce babu wanda zai zauna daga gidansa yana tsara yankin da APC za ta baiwa tikitin shugaban kasa a 2023 Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A cewar shugaban kasar, babu wanda zai zauna daga gidansa a Legas yana tsara wacce shiyya za a mikawa tikitin jam’iyyar, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Da yake ci gaba da magana, Buhari ya bayyana cewa kwamitin rikon kwarya na APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe na kokarin sake fasalin jam’ iyyar don mambobin su shiga cikin shawarar.

KU KARANTA KUMA: Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i

Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana mamakin yadda yan Najeriya suka amince suka zabeshi duk da cewa bai da kudi.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya karbi rahoton tsaro na taron matsalar tsaron da majalisar wakilai ta gudanar ranar 26 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya jagoranci tawagar yan majalisar wajen mikawa Buhari rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng