Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike
- Prince Uche Secondus ya ƙi yin musayar yawu da gwamnan jihar Ribas, Cif Nyesom Wike, wanda ya kira shi maƙaryaci kwanan nan
- Secondus, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party na kasa, ya bayyana cewa kiran mutum sunaye marasa dadi na daya daga cikin sadaukarwar shugaba
- An ruwaito cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban jam'iyyar PDP na kasa da Gwamna Wike a cikin 'yan kwanakin nan
Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Prince Uche Secondus, ya ce ba zai mayar da martani ga gwamnan jihar Ribas, Cif Nyesom Wike wanda ya kira shi da makaryaci ba.
Secondus ya ce jifarsa da Gwamna Wike yake yi da kalaman baki abu ne da zai ɗauka a matsayinsa na shugaba.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe
A ranar Asabar, 10 ga watan Yuli ne gwamnan jihar Ribas ya kira Secondus a matsayin maƙaryaci a Abuja yayin bikin cika shekaru 60 na tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Liyel Imoke.
Amma da yake martani ga harin da aka kaiwa Secondus, mai magana da yawun shugaban na PDP na kasa, Mista Ike Abonyi, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 13 ga Yuni, ya ce:
“Martaninmu shine cewa babu wani kalaman tunzura da zai sa Shugaban jam’iyyar na kasa ya kulla rigima da wani Shugaban jam’iyya balle ma a kai ga wani gwamnan jiha.
“Yin hakan shine cire rigar shugaban jam’iyyar. Tasirin irin wannan martani daga shugaban jam'iyyar na kasa kan jam'iyyar zai fi muni fiye da shiru.
"Shugaban jam’iyyar na kasa ya dauki duk wata mummunar magana da za a yi a kan sa daga kowane bangare a matsayin daya daga cikin nauyin shugabanci dole ne ya jure ya kuma ci gaba da samun karfin gwiwa musamman a lokacin da ba a gano gaskiyar cewa Secondus ba makaryaci ba ne."
Secondus ya mayar da hankali wajen wanzar da zaman lafiya a cikin PDP
Jaridar Nigerian Tribune a baya ta ruwaito cewa Secondus ya karyata cewar akwai rashin jituwa tsakaninsa da Gwamna Wike.
KU KARANTA KUMA: Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023
Shugaban na PDP ya bayyana cewa hasashen cewa dangantaka tayi tsami tsakaninsa da gwamnan jiharsa na iya batar da jama'a game da halin da jam'iyyar ke ciki.
A wani labari na daban, wani rahoto da ke fitowa ya nuna cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba ta yanke kowani shawara ba kan yankin da za ta mikawa tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba.
A cewar jaridar The Punch, majiyoyi da yawa daga PDP sun ce ya yi wuri da jam’iyyar za ta yanke hukunci a kan yankin da zai samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba.
Jaridar, ta bayyana cewa wasu mambobin jam'iyyar da suka yi magana ba tare da bayyana sunansu ba sun nuna bacin ransu game da batun mika mukamin shugaban kasa zuwa kowane yanki na kasar.
Asali: Legit.ng