Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

  • Farfesa Salisu Shehu, ya yi hira ta musamman da jaridar The Daily Reality
  • Malamin ya bada labarin zamansa Alkali a mukabalar da aka yi a makon jiya
  • Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya zauna da wasu malaman jihar Kano

Ya aka yi ka zama Alkalin zama?

“Ina so in yarda yin Ubangiji ne. Na san cewa an rubuta sunayen manya, dattawa, da muhimman mutane da za a tuntuba domin su yi wannan aiki, wasunsu sun ki yarda su yi, abin takaici kuma wasu ba su nan. Sunana ya na cikin wadanda aka bada, a karshe Allah ya yi cewa ni ne zan yi. Kwamitin ya yarda, don haka aka gabatar wa gwamnati da ni.”
"Ni karon kai na, na yi kokarin in ki karbar wannan aiki, amma kwamitin ya dage, ya sa na karba, tun da har gwamnatin jiha ta amince. Na karbi takarda, aka sa rana."

KU KARANTA: Tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara a muqabala

Kara karanta wannan

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

A game da dalilin sauran mutanen na kin karbar aikin saboda ganin bata lokaci ne a zauna da wanda ya zagi Ma’aiki SAW, babban malamin ya bada amsa cewa:

“Babu shakka wadannan munanan kalamai ne ake furta wa, kuma sauraronsu ya na da tashin hankali domin an ci mutuncin Annabi SAW ne. Amma idan aka duba bangaren larura a shari’a, dole ayi yunkurin da zai kawo karshen wannan lamari.”
“Na kuma ga yadda wannan mutum ya ke cika baki cewa duk abubuwan da yake fada gaskiya ne, kuma babu wanda zai iya fuskantar shi, shiyasa na ga bukatar in karbi wannan aikin, a yi wannan zama domin a kawo karshen duhun batar da ya shiga."

Korafin rashin isasshen lokaci

“Ba zai yiwu a zauna yin mukabala ba tare da kayyadajjen lokaci ba. Ba za mu zauna rana guda ayi ta tattauna wa ba, sai dai idan babu tsari, shi kadai yake kukan lokaci.”

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

KU KARANTA: Abduljabbar ya zauna da sauran Malaman Kano

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu
Salisu Shehu Hoto: dailyrealityng.com
Asali: UGC

“Kun ga yadda sauran malaman su ka bude litattafai kusan biyar a cikin mintuna gomansa. Abduljabbar ya na da komfuta ko wayar zamani, tare da dalibansa biyu. Menene aikinsu? Meyasa ya kawo su? Me zai hana su buda littafi kamar yadda aka nema?

Farfesa Shehu ya fada wa jaridar TDR sai da ya rika kai zuciya nesa domin gudun ransa ya baci a zaman.

Ku na da labarin cewa wasu daga cikin Almajiran Sheikh Abduljabbar Kabara sun soma canza layi. Sun fito Facebook suna bayyana cewa sun bar wannan tafiya.

Har an samu wani Sani Oris ya na barazanar kona masallacin Abduljabbar idan aka sake bude shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel