Kotu ta sanar da ranan sauraran karar da PDP ta shigar kan sauya shekar gwamna Matwalle
- Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta sanar da ranar da za ta saurari karar da aka shigar kan gwamna Matawalle
- Jam'iyyar APC ce daga jihar Zamfara ta kai karar gwamnan, tana mai neman kotu ta karbe kujerar gwamnan
- Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan na jihar Zamfara ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin ta sanar da 16 ga watan Yuli don sauraron karar da ke kalubalantar sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya yi zuwa Jam’iyyar APC, Daily Trust ta ruwaito.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya sanya ranar ne bayan ya saurari karar da lauyan masu shigar da kara, Kanu Agabi (SAN) ya shigar.
Mai shari'a Ekwo ya amince da rokon sannan ya dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Yuli.
KARANTA WANNAN: Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani
Karar da aka shigar tana dauke sunan wasu jiga-jigan PDP na Zamfara
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mambobin jam’iyyar PDP biyu daga jihar; Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed, a karar da ke da lamba: FHC/ABJ / CS / 489/2021, sun roki kotu da ta kori gwamnan kan sauya shekarsa, in ji rahoton The Nation.
Matawalle, APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) su ne wadanda ake kara daga 1 zuwa 4, yayin da PDP ta kasance cikin jerin jam’iyyun da za ta shiga cikin karar.
Masu shigar da karar suna kalubalantar cewa, saboda hukuncin da Kotun Koli ta yanke a baya, kan cewa APC ba ta da wani dan takara a zaben Gwamnan Jihar na 2019 a Zamfara saboda rashin gudanar da zaben fidda gwani ba.
Bisa wannan ya haramta ga Matawalle ya ci gaba da rike mukaminsa na ofisoshin gwamna da zarar ya fice daga PDP zuwa APC, ta hakan, ya mayar da nasarar PDP zuwa APC.
Suna son kotun ta bayyana cewa dole ne Matawalle ya yi murabus kafin sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
KARANTA WANNAN: ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya karbi bakuncin gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da takwaransa na jihar Kuros Riba, Ben Ayade, a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin.
Kwanan nan duka gwamnonin biyu suka fice daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ko da yake har yanzu ba a san cikakken bayani game da ganawar tasu ba, amma, an watsa hotuna a shafin Facebook na Gwamnatin Najeriya.
Asali: Legit.ng