Ministan Buhari ya kafa wa PDP hujja da shari'ar Atiku bayan ta fara shirin tsige Matawalle a kotu

Ministan Buhari ya kafa wa PDP hujja da shari'ar Atiku bayan ta fara shirin tsige Matawalle a kotu

  • Festus Keyamo ya yi tsokaci a kan sauya-shekar Bello Matawalle daga PDP
  • Ministan kwadago yace doka ba ta haramtawa Matawalle shigo wa APC ba
  • Keyamo SAN yace a doka, mai mulki zai iya canza jam’iyya bayan ya ci zabe

Karamin Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Festus Keyamo ya ce babu dokar da ta haramtawa Bello Matawalle sauya-sheka zuwa APC.

Festus Keyamo SAN ya fitar da jawabi a ranar 13 ga watan Yuli, 2021, inda yake cewa PDP ta na riko da hujjojin da ba za su yi mata aiki a gaban kotu ba.

Jam’iyyar PDP za ta shigar da kara a kotu, ta kalubalanci sauya-shekar da gwamna Bello Matawalle ya yi bayan zama gwamna a karkashinta.

KU KARANTA: APC ta dauki matakin da zai harzuka Jiga-jigan Jam'iyya a Zamfara

Keyamo wanda shi karon kansa lauya ne, ya ce riko da shari’ar Faleke da INEC da dogara da sashe na 221 na tsarin mulki ba za su ceci jam’iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

“Abin takaici ga PDP shi ne, hukuncin da kotun koli ta yanke a shari’ar Faleke da hukumar INEC bai shafi sauya-shekar gwamna zuwa wata jam’iyya ba.”
“Abin ban dariya ne sosai a ce PDP da ta yi murnar sauya-shekar gwamnan Benuwai, Samuel Ortom da gwamnan Edo, Godwin Obaseki daga APC, ta dage da karfin ta, ta na kokarin tsige Bello Matawalle saboda ya shigo jam’iyyar APC.”

This Day ta rahoto Ministan ya na cewa jam’iyya silar samun kujera ne, da zarar gwamna ya shiga ofis, zai iya barin jam’iyyar da ta kawo shi, ya canza-sheka.

Matawalle a Zamfara
Manyan APC da Matawalle a Zamfara Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ma'aikata za su sa rigar Adire Osun duk ranar Alhamis - Gwamna

“Ina mamakin karfin halin PDP da za ta umarci bankuna a kan cewa ka da su yi wata alaka da gwamnan da jama’a suka zaba. Abin ban dariya ne wannan.”

Babban laifi ne jam’iyyar hamayyar ta yi kokarin tsaida ayyukan komai a jihar Zamfara ba tare da samun takardar umarni daga kotu, ko dama a tsarin mulki ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Jaridar ta ce Keyamo ya tuna wa PDP shari’ar da aka taba yi a kotun koli, inda aka hana a taba kujerar Atiku Abubakar duk da ya sauya-sheka zuwa AC a 2007.

Wani babban kotun tarayya a Abuja ya sa rana domin a saurari karar da ke kalubalantar sauya shekar da Gwamna Bello Matawalle ya yi daga PDP zuwa APC.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya sanya ranar ne bayan ya saurari karar da lauyan masu shigar da kara, Kanu Agabi (SAN) watau PDP, ya shigar a cikin farkon makon nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel