Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

  • Mazauna jihar Sakkwato sun zargi wani mai suna Isma’il Isah da yin wasu kalamai da ake ganin ya saba wa addinin Musulunci
  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana matakan da aka dauka don magance matsalar
  • Ana daukar batanci ga Annabi a matsayin babban laifi a musulunci kuma yana da hukunci mai tsauri a karkashin tsarin shari'ar musulunci

An dan samu tashin hankali a jihar Sokoto a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuli, bayan zanga-zanga ta barke a jihar kan zargin kalaman batanci ga Annabi.

Masu zanga-zangar sun yi dafifi zuwa fadar Sarkin Musulmi, suna neman a hukunta wanda ake zargin, Isma’il Isah, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP na kudu maso gabas sun koma APC, an saki sunaye

Batanci ga Annabi: Tambuwal ya yi kira ga kwanciyar hankali, ya ce ana bincike kan mai laifin
Tambuwal ya ce ba zai lamunci rashin da'a ba Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya yi kira ga mutanen jihar da kada su tayar da hankali game da batun.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

Jami'an tsaro sun shigo ciki

Tambuwal a cikin wata sanarwa ta hannun kwamishinansa na yada labarai, Isah Galadanchi, ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na daukar matakan da suka dace don ganin an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Shari’a.

KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023

A cewar kafar yada labarai ta TVC News, ya yaba wa matasa a jihar kan yadda suka kai rahoton lamarin ga hukumomi a maimakon daukar doka a hannunsu.

Ya ce za a gabatar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace don fuskantar shari’a bayan an kammala bincike.

Hira da daya daga cikin jagororin zanga-zangar

Legit.ng ta zanta da mallam Abdullahi sa’i daya daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar da aka gudanar inda yace:

“Toh abunda za mu ce innalillahi wa’inna illaihi rajiun, domin irin wannan abun da ya faru ne abu ne na bakin ciki wanda duk wani Musulmi baya fatan ya ga irin wannan abun da idanun shi ko ya ji abun da kunnensa.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023

“A ce a samu mutum Musulmi yayi magana ta zagi, ya gunduma ashar zuwa ga ma’aiki SAW. Wannan abun bakin ciki ne ga Musulmin duniya baki daya.
“Abun da yasa mukayi hakan nan shine domin mutane abun ya musu zafi kuma sun fusata, don haka shi al’amari na addini dole ne a samu jagoranci shiyasa muka shigo muka jagorance su muka je har kofar gidan sarkin Musulmi domin nan ne gidan mujaddadi dan Fodio, nan ne fuska ta addini a Afrika ga baki daya, duk abun da ya taso na addini a nan ya kamata a fuskanta tunda matsala ce da ta shafi Shugaban halitta SAW, gidan sarki ya kamata a fuskanta kuma Allah ya sa mun je da matasa kuma an yi zanga-zanga ta lumana ba tare da an taba dukiya ko lafiyar wani ba ko an yi wani abu da bai dace ba.
“Da kuma muka je mun tarar da DPO na yan sanda yana a kofar gidan sarki wanda a nan suka tsaya suka yi magana da mu, muka gaya musu ga abun da muka zo yi ga korafinmu, ga matsalar da muke gani, wanda yake muna so mu san inda yaron yake da kuma halin da ake ciki, inda yace an kama shi."

Kara karanta wannan

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

Kan ko akwai wani wakili na sarki da ya fito yayi musu jawabi kan matakin da su za su dauka a matsayinsu na fada, Abdullahi ya ce:

“Shi DPO da shi muka yi magana bamu samu wani da ya fito ba kila saboda matsalar tsaro a kasar nan musamman manya duk abun da muka zo da shi tunda ba sanarwa muka yi za mu zo ba, mun fito ne kawai muka zo muka zagaya a gari muka zo kofar gidan sarki muka tsaya, amma dai bamu samu wani wakili a cikin gidan sarki wanda ya zo yayi mana jawabi ba. Dpo din ne dai ya zama kamar wakili na gidan sarkin."

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa wasu matasa a Sakkwato sun mamaye fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, suna neman a kama tare da gurfanar da wani Isma'ila Sani Isah na yankin Gobirawa.

Matasan dai suna zargin Isah da sanya kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a dandalinshi na sada zumunta ran laraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bayyana adadin mutanen da aka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2021

An tattaro cewa wanda ake zargin ya yi furucin ne domin nuna rashin amincewarsa da rashin samun aikin karamar hukuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel