Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari

  • Limamin coci ya yi kakkausar suka kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Ya koka game da yadda ya ce an mayar da al’ummar Ibo saniyar ware a harkokin mulkin kasar
  • A cewar limamin mutane na cikin kuncin rayuwa ta kowace fuska

Limamin majami’ar Nnewi Anglican Communion, Rabaran Ndubisi Obi, ya koka kan halin kuncin da 'yan Najeriya ke ciki, yana mai jaddada cewa mutanen yankin Kudu maso Gabas suna cikin bakar wahala da matsin da ba za su iya jurewa ba a karkashin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, game da taron addu’o’i na majami’ar Nnewi da ke tafe a harabar cocin da ke garin Nnewi, ya nuna damuwa game da yawaitar sace yara ‘yan makaranta da aika-aikar ‘yan bindiga da kashe-kashe da ma barnata dukiya da ke faruwa a kasar nan.

Taron addu’o’in za a gudanar da shi ne daga ranar 2 zuwa 5 ga watan Satumban da ke tafe a cocin St James Anglican, a Ichi da ke garin Nnewi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

Sannan ya yi nadamar yadda ya ce gwamnatocin tarayya da na jihohi da ma hukumomin tsaro, ba sa yin wani katabus domin taka wa lamarin birki.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin gwamnatin shugaba Buhari
Limamin coci ya koka kan wahalar da ‘yan Najeriya suke sha a karkashin mulkin Buhari Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

Mutan Najeriya na wahala

A cewar jaridar The Guardian, limamin cocin ya ce 'yan kasar na fama da yunwa da rashin aikin yi da tsadar rayuwa da dai sauran matsaloli yau da kullum daban-daban, sai dai a cewarsa duk da wadannan kalubalen rayuwar, mahukuntan ko a jikinsu.

Sannan ya zargi gwamnati da fifita kabilar Fulani a nade-naden mukaman gwamnatin.

Yace:

“Najeriya ba ta da shugabanci. Gwamnati ta gaza matuka. A wurina, Najeriya na samun koma baya maimakon ci gaba. Idan ka yi musu nasiha, sai su koma yi maka bita-da-kulli."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

Mutane a shirye suke su mutu kawai. Babu wani abu na daban.
Idan ka haifar da yanayi marar kyau, sannan mutane ba su gamsu da lamuran da ke tafiya ba, me kake tsammani ke nan daga gare su? Za ka shaida kwaramniyar fafutika.
“Jama’a a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da Midil Belt da mutanen kabliar Ijaw dukkaninsu kwaramniyar fafutika suke yi. Idan ka yi wa mutane a wannan gwamnati, kuma ba su saurare ka ba, me kake tsammani ke nan?”

Asali: Legit.ng

Online view pixel