Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP na kudu maso gabas sun koma APC, an saki sunaye
- Shugabannin jam’iyyar People Democratic Party (PDP) a kudu maso gabas suna yada zango a jam’iyyar APC gabanin zaben 2023
- Kimanin mambobin jam’iyyar adawa uku ne suka koma jam’iyya mai mulki a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli, a jihar Abia
- Masu sauya shekar sun koma jam’iyyar APC tare da wani tsohon dan takarar gwamna na SDP a jihar
Manyan mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Abia a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli, sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar All Progress Congress (APC).
Daga cikin wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki harda tsohon dan takarar gwamna na Social Democratic Party (SDP), Honarabul Blessing Nwagba, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023
Tsoffin jiga-jigan PDP da suka yanke hukuncin a ranar Juma’a su ne Arch Anagha Mba, Cif Silvanus Nwaji, Barr Chibuike Nwokeukwu (SAN), jaridar Guardian ta ruwaito.
Mutanen uku sun yi wa APC alkawarin za su yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar ta a zaben gwamna na 2023 a Abia.
KU KARANTA KUMA: An harbe wani dan siyasar Najeriya har lahira a wajen taron APC a Lagas
PDP ta sake rasa ɗan majalisar tarayya bayan ya koma APC
A wani labarin, Jonathan Gaza, ɗan majalisar wakilai na tarayya, ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya koma All Progressives Congress, APC, Premium Times ta ruwaito.
Premium Times ta ruwaito cewa gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya tafi majalisar domin halartar sauya sheƙan.
Asali: Legit.ng