Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

  • Matasa a Sakkwato sun gudanar da zanga-zanga a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar
  • Sun yi hakan ne a yayin da suke kira ga a kama tare da gurfanar da wani Isma'ila Sani Isah na yankin Gobirawa
  • An zargi matashin da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad

Wasu matasa a Sakkwato sun mamaye fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, suna neman a kama tare da gurfanar da wani Isma'ila Sani Isah na yankin Gobirawa.

Matasan dai suna zargin Isah da sanya kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a dandalinshi na sada zumunta ran laraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon yadda iyaye suka dungi kuka yayin da suka isa makarantar da ‘yan bindiga suka sace dalibai a Kaduna

Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi
Matasan sun nemi a hukunta wani da ake zargi da yin kalaman batanci ga Annabi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa wanda ake zargin ya yi furucin ne domin nuna rashin amincewarsa da rashin samun aikin karamar hukuma.

A cikin wallafar da aka ce yayi kamar yadda majiyarmu ta kawo, Isah ya zargi wani mutum a yankinsu da hana shi aikin duk da matsalar kudi da yake fuskanta.

Matasan wadanda ke dauke da kwalayen sanarwa inda wasunsu ke dauke da rubutu kamar "Muna kira ga majalisar masarautar ta dauki matakin da ya dace kan mai laifin" da kuma "dole ne Isma'il ya mutu" da sauransu sun kutsa cikin fadar da misalin karfe 5:00 na yamma.

KU KARANTA KUMA: Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari

Sai dai kuma, 'Yan sanda dauke da makamai a karkashin jagorancin babban jami'in' yan sanda na ofishin Marina, Cif Sufeto M Y Maru sun hana su shiga.

Maru yayin da yake magana da su, ya roke su da su kwantar da hankalinsu tunda wanda ake zargin yana tsare a sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

“Mun cafke wanda ake zargin. A yanzu haka yana tsare a ofishin CID kuma zan iya jagorantar shugabanninku zuwa babban ofishin don tabbatarwa,” inji shi.

A hedkwatar, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Abdullahi yayin karbar shugabannin matasa ya tabbatar musu da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun Shari’ah a ranar Litinin.

Ya yi kira gare su da kar su dauki doka a hannunsu.

Yawancin mazauna jihar sun koma dandalin sada zumunta domin yin Allah wadai da zargin da aka yi tare da wasu suna kira ga fille kan wanda yayi wallafar.

Hira da daya daga cikin jagororin zanga-zangar

Legit.ng ta zanta da mallam Abdullahi sa’i daya daga cikin wadanda suka jagoranci zanga-zangar da aka gudanar inda yace:

“Toh abunda za mu ce innalillahi wa’inna illaihi rajiun, domin irin wannan abun da ya faru ne abu ne na bakin ciki wanda duk wani Musulmi baya fatan ya ga irin wannan abun da idanun shi ko ya ji abun da kunnensa.
“A ce a samu mutum Musulmi yayi magana ta zagi, ya gunduma ashar zuwa ga ma’aiki SAW. Wannan abun bakin ciki ne ga Musulmin duniya baki daya.
“Abun da yasa mukayi hakan nan shine domin mutane abun ya musu zafi kuma sun fusata, don haka shi al’amari na addini dole ne a samu jagoranci shiyasa muka shigo muka jagorance su muka je har kofar gidan sarkin Musulmi domin nan ne gidan mujaddadi dan Fodio, nan ne fuska ta addini a Afrika ga baki daya, duk abun da ya taso na addini a nan ya kamata a fuskanta tunda matsala ce da ta shafi Shugaban halitta SAW, gidan sarki ya kamata a fuskanta kuma Allah ya sa mun je da matasa kuma an yi zanga-zanga ta lumana ba tare da an taba dukiya ko lafiyar wani ba ko an yi wani abu da bai dace ba.
“Da kuma muka je mun tarar da DPO na yan sanda yana a kofar gidan sarki wanda a nan suka tsaya suka yi magana da mu, muka gaya musu ga abun da muka zo yi ga korafinmu, ga matsalar da muke gani, wanda yake muna so mu san inda yaron yake da kuma halin da ake ciki, inda yace an kama shi."

Kan ko akwai wani wakili na sarki da ya fito yayi musu jawabi kan matakin da su za su dauka a matsayinsu na fada, Abdullahi ya ce:

“Shi DPO da shi muka yi magana bamu samu wani da ya fito ba kila saboda matsalar tsaro a kasar nan musamman manya duk abun da muka zo da shi tunda ba sanarwa muka yi za mu zo ba, mun fito ne kawai muka zo muka zagaya a gari muka zo kofar gidan sarki muka tsaya, amma dai bamu samu wani wakili a cikin gidan sarki wanda ya zo yayi mana jawabi ba. Dpo din ne dai ya zama kamar wakili na gidan sarkin."

Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka

A wani labarin, kasar Amurka ta bayyana damuwarta kan yadda kotuna a Najeriya ke cigaba da hukunta masu laifin batanci ga Annabi, ta hanyar jefasu kurkuku da yanke musu hukuncin kisa.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rahoton yancin addini na 2020, rahoton Punch.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya har yanzu bata hukunta wadanda suka hallaka mambobin kungiyar Shi'a da aka yiwa kisan gilla a shekarar 2015 ba amma tana hukunci masu laifin batanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel