Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa
- Manyan masu ruwa da tsaki na APC da dama sun yi amannar cewa Sanata Sani Mohammed Musa dan siyasa ne da ya cancanci maye gurbin Adams Oshiomhole
- Wannan shine dalilin da ya sa jiga-jigan jam'iyyar suka yi kira ga takwarorinsu da su marawa dan majalisar na Neja baya
- Mambobin APC da ke son Musa ya zama shugaban jam’iyyar na kasa na gaba sun ce yana da kyawawan bayanai a matsayin jagora
Mambobin wata kungiya a cikin jam’iyya mai mulki sun nuna goyon bayansu ga Sanata Sani Musa, wanda ke wakiltar yankin Neja ta gabas a majalisar dokokin tarayya don ya zama shugaban APC na kasa.
A cewar jagororin kungiyar, Yemi Adeleye da Sabiu Ali, Musa na da damar hada kan mambobin APC da suka fusata tare da saita jam’iyyar zuwa ga cin nasara a zabukan shekarar 2023, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin
A wata sanarwa da su biyun suka fitar, sun bayyana dan majalisar dattijan na arewa a matsayin dan siyasa wanda ya samu kwarewar jagoranci daga bangaren kasuwanci da kuma bangaren majalisa don haka ya dace da kujerar.
Sun yi iƙirarin cewa APC na buƙatar irin su Sanata Musa don ci gaba da sulhu da sake dawo da zaman lafiya na kwamitin rikon kwarya da Mai Mala Buni ke jagoranta, Leadership ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP na kudu maso gabas sun koma APC, an saki sunaye
Jawabin ya ce:
“Wannan lokaci ne da APC za ta samu mutum irin Sanata Mohammed Sani Musa a matsayin Shugaban Jam’iyyar na kasa don jagorantar lamuran jam’iyyar zuwa nasara a 2023 da bayanta.
“Sanatan ya kasance amintacce kuma wanda zai shawo kan matsaloli a dukkan matakai.”
A wani labari na daban, wani rahoto da ke fitowa ya nuna cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba ta yanke kowani shawara ba kan yankin da za ta mikawa tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba.
A cewar jaridar The Punch, majiyoyi da yawa daga PDP sun ce ya yi wuri da jam’iyyar za ta yanke hukunci a kan yankin da zai samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba.
Jaridar, ta bayyana cewa wasu mambobin jam'iyyar da suka yi magana ba tare da bayyana sunansu ba sun nuna bacin ransu game da batun mika mukamin shugaban kasa zuwa kowane yanki na kasar.
Asali: Legit.ng