Gwamnoni sun bayyana adadin mutanen da aka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2021

Gwamnoni sun bayyana adadin mutanen da aka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2021

  • Kungiyar Gwamnoni na kasa sun koka game da matsalar tsaro a Najeriya
  • Shugaban NGF, Kayode Fayemi ya ce mutane 76, 000 aka kashe daga 2011
  • Gwamnan Gwamnoni ya bayyana cewa an daina imani da aikin Gwamnati

Kungiyar gwamnonin Najeriya na NGF ta ce tsakanin watan Mayun shekara 2011 zuwa Fubrairun shekarar nan ta 2021, an kashe mutane fiye da 76, 000.

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni na kasa ya bayyana wannan a Abuja.

Kayode Fayemi ya yi wannan bayani ne a wajen taron Peace and Inclusive Security Initiative da kungiyar gwamnonin na NGF su ka shirya a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Sunday Igboho zai yi shari’a da Gwamnatin Buhari

Gwamnonin Jihohi
Kungiyar NGF Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Gwamnonin sun kawo tsarin Peace and Inclusive Security Initiative domin a yi maganin matsalar tsaro.

NGF ta ce bayan barkowar makamai a Najeriya, akwai yawan rikicin kabilanci da ake fama da shi wanda hakan ya yi sanadiyyar dinbin mutane a kasar nan.

Kara karanta wannan

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

A jawabin na sa, Dr. Fayemi ya kuma nuna takaicinsa a game da yadda matsalar tsaro ta ke neman ta addabi Najeriya, ta hana al’umma fita neman na abinci.

KU KARANTA: Ingila za ta binciki yadda Gwamnatin Buhari ta kudunduno Kanu

Kungiyar ta NGF ta bakin shugabanta, ta ce halin rashin tsaro da kashe-kashen da ake fuskanta, ya zama barazana ga hakkin da ‘yan kasa su ke da shi a doka.

Wani darekta a ofishin cigaban kasashen renon Birtaniya, Foreign, Commonwealth & Development Office, ya ce za a iya samun matsala a zaben 2023.

Idan za ku tuna, Christopher Pycroft ya bayyana wannan ne ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2021, wajen kaddamar da shirin PISI da gwamnoni su ka fito da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng