MSF: Wasu Musulmai sun ce Hassan Kukah ya bada hakuri ko ya tashi daga jihar Sokoto

MSF: Wasu Musulmai sun ce Hassan Kukah ya bada hakuri ko ya tashi daga jihar Sokoto

- Kungiyar Muslim Solidarity Forum ta ragargaji Mathew Hassan Kukah

- Musulman sun fusata da wasu kalaman da Faston ya yi a bikin kirismeti

- Ana zargin Kukah da jawo rikici, an bukaci ya nemi afuwa ko ya yi kaura

Babban faston darikar Katolika a kasar Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya na fuskantar barazana bayan jawabinsa da ya yi na bikin kiremeti a 2020.

Kungiyar al’ummar Muslimi ta bukaci faston ya fito ya bada hakuri game da kalaman da ya yi, ta ce idan ba haka ba, ya yi gaggawa ya bar jihar Sokoto salin-alin.

Wata al’ummar musulmai da ke Sokoto sun fadawa Mathew Hassan Kukah ya daina sukar musulunci da kuma musulmai, Punch ta fitar da wannan rahoto.

Wannan magana ta fito ne daga kungiyar Muslim Solidarity Forum ta reshen jihar Sokoto a wani jawabi da ta fitar ta bakin mukaddashin shugabanta.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

KU KARANTA: Hukumar DSS ta damke masu shirya zanga-zanga a Kano

Farfesa Isa Maishanu ya maidawa Rabaren Mathew Kukah martani na jawabin kirismetin da ya yi, inda ya ce yana kokarin hada musulmai da kiristoci fada.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Muslim Solidarity Forum ta ce malamin addinin kiristan ya na wasa da karar da ake yi masa a Sokoto, har ta kai ya koma sukar musulmai bini-bini.

Kungiyar ta ce a 2020, Kukah ya jagoranci zanga-zanga na kisan wani Fasto a Sokoto, amma ya yi gum game da tarin Fulani da aka kashe a Taraba a 2018.

Maishanu ya tunawa Kukah abin da aka yi wa Musulmai a Kafanchan a 1987, Zango Kataf a 1992, Tafawa Balewa a 1991, 1993, 1995 da 2001, da Yelwa Shandam a 2004, da kuma Zonkwa da Jarkasa a 2011?”

Kara karanta wannan

Yadda Kwanturolan Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano

KU KARANTA: DSS ta binciki Faston da yace Buhari ya mutu

MSF: Wasu Musulmai sun ce Hassan Kukah ya bada hakuri ko ya tashi daga jihar Sokoto
Bishof Hassan Kukah Hoto:www.vanguardngr.com/2020/12/i-didnt-call-for-coup-kukah
Asali: UGC

Wannan kungiya ta Muslim Solidarity Forum ta nemi Faston ya nemi afuwar jama'a, ko ya fice daga Sokoto gaba daya.

Hakan na zuwa ne bayan jami’an DSS sun ce sun bankado yunkurin kawo rikicin addini a wasu jihohi.

A wata sanarwa da ta fitar kwanan nan, hukumar DSS ta ce ta fahimci akwai yunkuri da wasu jama'a ke yi na tada rikicin addini a kasar nan.

An ambaci jihohin Sokoto, Kano, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo, da kuma jihar Legas a cikin wuraren da ake shirin tada zaune-tsaye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng