Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

  • Bayan an gama kai-komo, an gurfanar da Hon. Linus Okorie a gaban wani kotun majistare a Ebonyi
  • Alkali ta saurari zargin da ake yi wa Okorie, ta kuma bada umarnin a tsare ‘dan takaran a kurkuku
  • Lauyan Okorie yace ana yi masa haka ne saboda yana takara da Mai girma Gwamna David Umahi

Ebonyi - Wani kotun majistare mai zama a jihar Ebonyi, ya bada umarni a tsare Hon. Linus Okorie a gidan gyaran hali na babban birnin Abakaliki.

The Cable a rahoton da ta fitar a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba 2022, tace ana tuhumar Linus Okorie da hannu wajen kisan kai a kwanaki.

Kakakin ‘yan sanda na Ebonyi, Chris Anyanwu ya fitar da jawabi na musamman a farkon makon nan, yana bayanin tuhumar da ake yi wa Okorie.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

A cewar Anyanwu, baya ga zargin harkar miyagun kwayoyi da ake yi wa ‘dan takaran, ana zargin yana da hannu a rikicin da aka taba yi a Onicha.

Kisan kai da yi wa Gwamna kazafi

Tun shekarar 2021 rigingimu suka barke a yankin Onicha, wanda hakan ya yi sanadiyyar da ‘yan bindiga suka jawo aka rasa rayukan Bayin Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an ‘yan sandan jihar Ebonyi sun ce ana zargin Hon. Okorie da laifin yada labaran karya a kan Gwamna Umahi, wanda yin hakan laifi ne.

Hon Linus Okorie
Hon Linus Okorie Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Dailypost tace laifuffuan da ke wuyan tsohon ‘dan majalisar sun hada da hannu a kisan kai da jawo rikicin kabilanci da sun sabawa dokar jiha.

Lauya ya musanya zargin

Lauyan da ya tsaya masa, Chikodili Nome yace ana tuhumar Okorie da wadannan laifuffuka ne saboda a garkame shi, a karya magoya bayansa.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP ya Raba Kayan Tallafin Ga Wadanda Masifa ta Auka Masu

Nome yake cewa akwai umarnin da Alkalin babban kotun tarayya ya bada, inda ya haramtawa ‘yan sanda da gwamnati taba wanda ake tuhuma.

Mai shari’a Linda Ogodo tace ba ta da karfin da za ta saurari wannan shari’a, sai ta bada umarnin a rufe Okorie a kurkuku kafin a yanke shawara.

Sai zuwa 4 ga watan Nuwamban 2022 za a koma kotu domin a cigaba da wannan shari’a.

An yi garkuwa da Okorie da Onicha?

A farkon makon nan, rahoton da aka ji shi ne ana zargin miyagun ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Ohaozara Onicha da Linus Abaa Okorie a Ebonyi.

A halin yanzu ‘dan siyasar yana neman kujarar Sanatan Ebonyi ta Kudu a majalisar dattawa, yana takara da Gwamna mai-ci, David Umahi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel