Yadda Kwanturolan Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano

Yadda Kwanturolan Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano

  • Mr Anthony Ayalogu, kwanturola mai kula da sashin cinikayya a Hukumar Kwastam ta Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
  • Ayalogu, dan asalin karamar hukumar Onitsha ta Arewa a Jihar Anambra ya rasu ne bayan yanke jiki ya fadi a filin jirgin
  • Hamid Ali, Kwanturola Janar na Kwastam ya ya alhinin rasuwar Ayalogu ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin

Kano - Kwantrola mai kula da sashin cinikayya ta Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, Anthony Ayalogu, ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta rahoto.

Ayalogu ya mutu ne a filin tashi da saukan jiragen sama na kasa da kasa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano, sakamakon rashin lafiya.

Ayalogu
Kwanturola Na Kwastam Ya Yanke Jiki Ya Mutu A Filin Jirgin Sama A Kano. Hoto: @Daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da sashin hulda da jama'a na kwastam ta fitar, AA Maiwada, ya ce bayan Ayalogu ya dena numfashi, an garzaya da shi asibitin Rundunar sojojin saman da ke Kano inda aka tabbatar ya rasu.

Yadda Ayalogu ya rasu

Ya ce:

"Yana kan hanyarsa ne zuwa wani aiki nan take ya kamu da rashin lafiya bayan ya iso filin jiragen sama na Malam Aminu Kano kuma ya yanke jiki ya fadi sumamme.
"An yi dukkan kokarin farfado da shi amma ba a yi nasara ba kuma an sanar ya mutu misalin karfe 8.20 na daren ranar Litinin 17 ga watan Oktoban 2022 a Asibitin 465 ta Rundunar Sojojin Saman Najeriya a Kano. Shekarunsa 57."

Hamid Ali ya yi ta'aziyya ga iyalan Ayalogu

A cewar Maiwada, Kwantrola Janar na Kwastam, Kwanel Hamid Ali (mai ritaya), yayin mika ta'ziyya ga iyalansa ya ce za a yi kewansa sosai.

An ambato Ali yana cewa:

"Muna addu'a Allah ya bawa iyalan Ayalogu hakurin jure rashinsa."

Ayalogu, dan asalin karamar hukumar Onitsha ta Arewa ne a Jihar Anambra, ya yi karatun digiri a bangaren nazarin tsirai (Botany) daga Jami'ar Port Harcourt, Jihar Rivers.

Ya fara aiki da NCS a ranar 24 ga watan Satumban 1991 a matsayin Mataimakin Sufritanda.

Gogaggen Dan jarida, Mallam Abdulhamid Agaka Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani rahoton, gogaggen dan jarida kuma kwararre a bangaren kafar watsa labarai, Mallam Abdulhamid Agaka, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton Leadership.

A cewar kafar watsa labarai ta PRNigeria, dan jaridar wanda matarsa da mutu a makon da ya wuce, ya mutu cikin barcinsa a daren ranar Laraba a gidansa da ke Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel