Sunayen jihohi 7: DSS ta bankado yunkurin tada rikicin addini a wasu jihohi

Sunayen jihohi 7: DSS ta bankado yunkurin tada rikicin addini a wasu jihohi

- Hukumar DSS ta bankado wani yunkuri da wasu jama'a ke yi na tada rikicin addini a kasar nan

- Suna kokarin tada rikicin a jihohin Sokoto, Kano, Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos and wasu na kudu maso gabas

- Kamar yadda hukumar ta sanar, tana kokari tare da wasu cibiyoyin tsaro wurin tabbatar sun shawo kan lamarin

Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya ta bayyana cewa wasu mutane na kokarin tada rikicin addini a kasar nan a kowanne lokaci daga yanzu.

Amma a wata takarda da ta fito daga hannun kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa jami'ansu suna kokarin shawo kan lamurran domin bai wa 'yan Najeriya kariya.

Takardar wacce jaridar Vanguard ta gani a ranar Litinin, ta lissafa jihohin da masu son tada tarzomar suka mayar da hankali.

Sun hada da jihohin: Sokoto, Kano, Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos and wasu na kudu maso gabas.

KU KARANTA: Hotunan direbobin tifa suna toshe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto, sun sanar da dalili

Akwai masu yunkurin tada rikicin addini a Najeriya, DSS
Akwai masu yunkurin tada rikicin addini a Najeriya, DSS. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Takardar ta ce: "Hukumar tsaro ta farin kaya tana sanar da mutane cewa wasu miyagu suna kokarin tada tarzomar addini a fadin kasar nan.

"Wuraren da suke duba sun hada da jihohin Sokoto, Kano, Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos ada wasu a kudu maso yamma.

"Daga cikin shirinsu shine yin amfani da sahun sojoji wurin harar wuraren bauta, shugabannin addinai, manyan mutane da sauransu.

"A don haka ake shawartar 'yan Najeriya da su kasance masu gujewa irin wadannan mutane.

"Yayin da hukumar take kokarin ganin ta hada kai da sauran hukumomin tsaron wurin tabbatar da zaman lafiya, tana shawartar masu wannan yunkurin da su guji aikata hakan domin tabbatar da zaman lafiya.

"Amma kuma ana shawartar 'yan kasa nagari da kuma sauran jama'a da su kai rahoton duk wani karantsaye na zaman lafiya ga hukumar tsaro mafi kusa," Hukumar tace.

KU KARANTA: Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu

A wani labari na daban, wata matashiya mai bautar kasa a jihar Akwa Ibom ta sha duka kamar bakuwar karya a ranar Lahadi. Baya ga dukan, har tsirara wasu samari suka yi mata, suna zarginta da kashe wani mutum bayan ya kwana da ita.

An ga bidiyon matashiyar, mai suna Odume Paschaline, ta kammala karatunta a jami'ar Najeriya dake Nsukka, tsirara haihuwar uwarta, maza suna dukanta da kuma zaginta. Alamu sun nuna a tsakar anguwa ne al'amarin ya faru.

A wani bidiyo da aka tura wa Premium Times ta WhatsApp, wanda wani mutum da lamarin ya faru gaban shi ya kwashe tas a wayarsa, an ga yadda samarin suka tozarta budurwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel