Da duminsa: Hukumar DSS ta damke masu shirya zanga-zanga a Kano

Da duminsa: Hukumar DSS ta damke masu shirya zanga-zanga a Kano

- Hukumar DSS ta gayyaci manyan shugabannin gamayyar kungiyoyin Arewa CNG

- Gamayyar ta shirya gudanar da zanga-zanga a yankin Arewacin Najeriya

- Maimakon na #ENDSARS da ake a kudu, na Arewa na shirin na su kan rashin tsaro

Hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta tsare masu shirya zanga-zangar yunkurin kawo karshen "rashin tsaro da mulkin kwarai."

A jawabin da kakakin gamayyar kungiyoyin arewa CNG, AbdulAzeez Suleiman, ya saki ranar Asabar kuma TheCable ta samu, ya ce an tsare wasu mambobinsu da aka gayyata ofishin hukumar ta DSS domin yi musu tambayoyi amma aka tsaresu daga baya.

Ya ce wadanda aka tsare sune Nastura Sharif, Balarabe Rufai, Aminu adam da Muhammad Nawaila.

"Zanga-zangar #EndInsecurityNow kan matsalar kashe a arewacin Najeriya da koran mutane da muhallinsu ta fara fuskantar barazana daga DSS da ta lashi takobin toshe muryar dan Arewa, " yace.

"Yanzu hukumar DSS ta gayyaci shugabannin CNG, Nastura Sharif, Balarabe Rufa'i, Aminu Adam da Dr Muhammad Nawaila a Kano, inda aka rike su daga karfe 11 na daren Juma'a zuwa 2:15 na safiyar Asabar.

"Tun daga lokacin da aka tsaresu a Ofishin DSS, ba'a samu yin magana da su ba, ba su amsa wayoyinsu." ya kara.

KU KARANTA: Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

Da duminsa: Hukumar DSS ta damke masu shirya zanga-zanga a Kano
Da duminsa: Hukumar DSS ta damke masu shirya zanga-zanga a Kano
Asali: Facebook

KU DUBA: Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi

A bangare guda, rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) karkashin atisayen Operation LAFIYA DOLE sun samu nasarar ragargaza wani sansanin yan ta'addan Boko Haram da ISWAP dake yankin tafkin Chadi a Borno.

Jami'an sun samu nasarar yin hakan ne a harin da suka kai ranar Alhamis, 15 ga Oktoba.

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa "rundunar sojin sun kashe yan ta'addan ISWAP da dama kuma suka ragargaza sansaninsu dake Tudun Wulgo da Tumbin Gini dake yankin tafkin Chadi dake jihar Borno."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng