Limamin coci ya shiga uku hannun DSS bayan fadar Aso Rock ta sami labarin yana cewa Buhari ya mutu
- Shugabancin kasa ta bukaci DSS da 'yan sandan Najeriya dasu binciki Bishop Eze Orieke
- An zargi Bishop din ne da yada jita jitan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu
- Har ta kai ga yana yada takardun bogi a dandalin sada zumunta na mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ofishin shugaban kasa ya rubuta ga DSS da 'yan sandan Najeriya domin bukatar bincikar Bishop Oze akan zargin shi na yada jita jitar mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mataimakin shugaban kasa na musamman akan kararraki ne ya mika karar ga Daraktan DSS, Yusuf Bichi da sifeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris, kamar yanda majiyar mu ta sanar damu.
Wasikar ta kunshi sunan Bishop Eze Orieke, tare da karawa da cewa yana yada cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu tare da wasu takardun bogi daga London Bridge Hospital a shafin shi na Facebook mai suna 'Zauren siyasar Ohafia'
DUBA WANNAN: Farashin abinci ya sauko
"Ga takardun nan tare da Wasikar. Wannan abun mamaki ne baya da munsan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiyar shi kalau yana harkokin shi, " inji Obono - Obla, Editan Wasikar.
Takardun na bogi ne kuma suna tsoratarwa tare da kawo nakasu a tsaron kasar.
A tare da Wasikar akwai shaidar cewa shugaban kasa ya rasu sakamakon ciwon zuciya a garin Abuja a ranar 19 ga watan Satumba, wanda kamashon kidaya na kasa ya bada.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng