'Yan Fashi Sun Shiga Gidan Aubameyang, Sun Lallasa Shi tare da Masa Sata

'Yan Fashi Sun Shiga Gidan Aubameyang, Sun Lallasa Shi tare da Masa Sata

  • 'Yan fashi da makami sun shiga gidan zakaran kwallon kafa na Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang
  • Kamar yadda aka gano, sun shiga gidan da bindigogi da sandunan karfe bayan sun haura ta lambun dake bayan gida
  • Sun yi barazana ga matarsa da shi kansa inda suka tirsasa bude ma'adanarsu kuma suka kwashe kayan karau

Zakaran kwallon kafa na kungiyar Barcelona, Pierre-Emerick Aubameyang, ya shiga tashin hankali bayan 'yan fashi da makami sun kutsa gidansa a sa'o'in farko na ranar Litinin, cewar kungiyar kwallon kafan ta Spain.

Aubameyang
'Yan Fashi Sun Shiga Gidan Aubameyang, Sun Lallasa Shi tare da Masa Sata. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

"A halin yanzu yana lafiya amma a tsorace," wata majiya daga Barcelona ta sanar da AFP yayin tabbatar da rahoton manema labarai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalla 'yan fashin hudu ne suka kutsa gidansa dake Castelldefels kusa da Barcelona ta lambunsa inda suka yi barazana garesa da matarsa da bindigogi da sandunan karfe, Daily El Pais suka rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Daba Sun Kone Gidan 'Yan Shi'a, Kadarorin N3m Sun yi Kurmus

Barayin sun tsere da mota bayan sun tirsasa zakaran kwallon kafan 'dan asalina kasar Gabon da ya bude ma'adanarsa kuma suka kwashe kayan karau.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, mai magana ya yawun 'yan sandan Catalan, the Mossos d’Esquadra, ta tabbatar da cewa sun bincike kan fashin da aka yi a Castelldefels amma ta ki bayyana sunan wanda aka yi wa fashin.

"Har a yanzu a bude yake binciken kuma muna tattara bayanai ne," ta sanar da AFP.

Jarumin Kwallon Kafa Ahmed Musa Da Mai Dakinsa Sun Samu Karuwar Da Namiji

A wani labari na daban, Allah ya azurta Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa tare da matarsa da samun karuwar 'da namiji.

Dan wasan kwallon kafar ya je shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, domin sanar da wannan abun alkhairi da ya samu iyalinsa.

Yayin da yake hamdala ga Ubangiji a kan wannan babban kyauta da ya yi masa, dan wasan ya bayyana sunan jinjirin a matsayin Adam Ahmed Musa amma za a dunga kiransa da Zayd.

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Tuni masoya da abokan arziki suka cika bangaren da aka tanada don sharhi don taya shi murnar wannan babban arziki da Allah ya yi masa a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel